GUZIRIN MAI HAILA

GUZIRIN MAI HAILA KASHI NA BIYAR

Sponsored Links

                       بسم الله الرحمن الرحيم

(7) LOKUTAN DA BAI WAJABA MAI HAILA TA RAMA SALLAH BA.

a- Idan jini yazowa mace kafin rana ta fadi misalin saura minti biyar rana ta fadi sai jini ya zowa mace to bayan jinin ya dauke mata ba zata rama azahar ba la’asar ba magariba da isha ba.

b-hakanan idan jini yazowa mace kafin alfijr ya keto misalin ace saura minti hudu ya keto sai jini yazo mace baza ta rama magariba da isha ba sai dai indai sakaci tayi sai ta rama.

                        (8) WANKA

   Yadda ake wankan haila kamar wankan janaba yake, kawai sai bambancin niyya, amma niyya a zuci akeyi, ga yadda ake wankan.

  Da farko za ‘a samo ruwa mai tsarki kamar yadda aka sani, ruwa mai tsarki shine wanda kamar sa ba canza ba, ko dan – danon sa ko kashin sa. to in an sami wannan ruwa sai kiyi niyya ki fara wanke hannayenki ba a cikin abin wanka ba.
    sannan ki wanke gabanki zuwa cinyoyin ki. sai ki wanke kanki sau idan kitson da ake tamke wa da roba ne sai kin warware shi {dole}, saboda ruwa ba zai shiga ba sai kin warware kitson ki, sai kifara wanke bangaren jikin ki na dama sannan na barin hagu shima kamar haka kuma ki kula da matse matsin jikin ki kamar Kasan haba da kasan nono ko tsakiyar cinya ko hammata da dai sauran su sannan ki wanke jikin ki gaba daya sosai. Allah masani.

                   (9) FA’IDOJI

   1- Misali idan mace tana hailar kwana uku a wata sai wani watan ya zama tayi kwana ukun bai tsaya ba to sai kara kwana uku a wannan watan, daga haka in bai tsaya ba sai wanka ta cigaba da sallah, amma bazata sake kara ukun ba a wannan watan, domin ya za jinin cuta kenan ba wai ana nufin in ta kara ukun bai tsaya ba tsaya ba tayi ta kara ukun bane a’a in ta kara ukun sau daya shike nan.

 2- Idan haila ta sami mace a makka tana tsaka da aikin Hajji dukkan komai na aikin hajji za tayi banda dawafi amma in ya zama za’a kwashe su daga makka zuwa kasar su jini kuma bai dauke ba kuma gashi ba tayi dawafin wajibiba to malamai sun ce ta iya shan magani domen jini ya tsaya domin tayi dawafin ta na wajibi.
   Amma idan dawafin farko ne ko kuma dawafin ban kwana to ba bu komai in bata yi ba. Amma ki sani shan magani yana da hadari wannanmma sabo da lurura ne kawai.

3- Idan Mace ba ta iya gane yanyin jininta bakine ko ja sai ta zauna tsawo kwana shida ko bakwai wato kwana shida ko bakwai shi zata kirga amadadin hailarta. domin Bukhri ya rawaito daga nana Aisha cewa, Fadima ‘yar Abi hubaishin tace wa Annabi ( S. A. W) : nifa kullum cikin jini nake wato bata gane Al-darta sai yace kiyi sallah kwana ashirin da uku ko da hudu saran kwanaki shida ko bakwai shine kwanaki hailarki duk wata sauran jinin da kike gani zungurar shedan ne yake taba jijiya.

4- Idan kuma jinin wataran taga baki wataran taga ja to zata lissafa bakin shine jinin haila.

5- Mata su sani in sun sami tsarki zasu wanke gaban su baza ‘ a zura dan yatsa ba saboda yana cutarwa kadan daga ciki yana rage jin dadi wajen sasduwa.

 6- Wasu sun ce mace tana fara haila ne tana’ yar shekara tara har zuwa shekara hamsin, darima yace zata iya haila tana ‘yar shekara tara ko kafin ta kai taran ko bayan shekara hamsin zata iya cigaba da haila ya dangata da yana yinda take ciki ko kasar da take ciki.

                             وبالله التوفيق

DAGA DALIBINKU
  MUSA S ZAGE 

Leave a Reply

Back to top button