Dabarun Rubutun Waka

YADDA AKE RUBUTUN WAKOKIN HAUSA. by MSZ.

Sponsored Links
     DABARUN RUBUTUN WAKOKI
   
PART 4  
  Daga      
Nasir G Ahmad 
RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA 
  Assalamu alaikum.       
A makon jiya mun duba yadda marubucin waka kan samu ne. Amma kamata ya yi kafin nan mu yi dan gajeren bayani kan tarihi samuwar rubutattun wakokin. Don haka yau za mu yi kara’i ne.
ASALIN RUBUTATTUN WAKOKIN HAUSA.
Rubutattun wakokin Hausa sun samo asali ne daga rubutattun wakokin Larabci, wadanda malaman kasar Hausa na dauri suka nazarta don kara fahimtar luggar Larabci wadda za ta zame musu jagora wajen fahimtar Alkur’ani da sauran fannonin ilimin addinin musulunci, al’amarin da ya kai su ga kwaikwayon wakokin (na Larabci), suna rubuta nasu kan wa’azi da fadakarwa da ilmantarwa cikin harshen Larabci.

 Da suka nuna a fagen rubuta wakokin Larabci da ilimin awon waka (Aruli), sai kuma suka shiga wallafa wakoki cikin harsunanmu na gida, kamar Fulatanci da Hausa, bisa zubi da tsari da sauran ka’idojin wakokin Larabci.
Tun cikin karni na goma sha bakwai ake hasasashen an fara rubuta wakar Hausa, inda aka binciko wata wakar Wali dan Masani, wanda ya yi zamaninsa a kasar Katsina, mai suna “Wakar Yakin Badar.” Amma habaka da bunkasa da shaharar rubutattun wakokin Hausa sun samu ne cikin karni na goma sha Tara, lokacin wa’azi da jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo da sahabbansa, inda masu jihadin suka wallafa wakoki masu tarin yawa cikin harsunan Hausa da Fulatanci, don wa’azi da fadakarwa koyar da ibada, wadanda almajiransu kan juya su haddace, suna rerawa a wuraren wa ‘azi. Jigogin rubutattun wakokin Hausa a wancan lokaci duk na addini ne. Sun kuma rubuta wakokin nasu ne cikin rubutun ajamin Hausa.

<

Bayan zuwan Turawa da samuwar rubutun boko a karni na ashirin ne, aka fara samun sabbin jigogi na rubutattun wakokin Hausa, kamar siyasa, tafiye-t deafiye, soyayya, da makamantansu. A wannan karni na ashirin da daya da muke ciki kuma, aka kara samun sauye-sauye a rubutattun wakokin Hausa wajen zubi da tsarinsu, salon aiwatar da su, da hada su da kida.

anan zamu diga aya sai muhadu a Kashi na gaba
   Daga naku.                             
  musa s Zage
                    
 Tsangayar da ta himmatu wajen kulawa da killacewa da taskace abubuwan da suka shafi adabi da zamantakewar al’ummar hausawa.

Leave a Reply

Back to top button