Labarai

Hajjin bana akwai abin da mahajjatan duniya za su yi kewar su a Hajjin bana Sama da guda 20!.

Sponsored Links

 Daga naku 

musa s zage

 Zaman Muzdalifa na cikin manyan abubuwan da Mahajjatan wannan shekarar za su yi kewarsa .

A daidai irin wannan lokaci a kowace shekarar Musulunci, miliyoyin Musulmai ke taruwa a kasa mai tsarki don gudanar da ibadar aikin Hajji, wacce daya ce daga cikin rukunan addinin.

 Sai dai a wannan shekara al’marin ya sha bamban, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, annobar cutar korona Karo na biyu ta hana Musulmai daga sauran kasashen duniya samun damar yin aikin.

DOMIN KALLON RANAR ARFAT NOW 

 Play now

1.Hawan Arfa Hawan Arfa shi ne jigo na aikin Hajji, wanda idan babu shi to hajjin ba ta kammaluwa. 

Ana yin hawan Arfa ne a ranar 9 ga watan Zul Hijja, inda a kan fita tun kafin ko bayan sallar Asuba. Ana dai so a fita kafin rana ta fito. 

Mahajjata na wuni zur a wajen suna gabatar da adduóí da zikirai da karatun kuráni. A kan bar filin Arfah kafin rana ta fadi.

 Hakika yinin filin Arfa na sanya nutsuwa a zukatan masu ibada, don haka dole mahajjatan da suka yi niyya bana su ji ina ma a ce suna can su samu albarkar wannan yini. 

2.Kwanan Muzdalifa Filin Muzdalifa shi ne wajen da alhazai ke wucewa bayan an sauka daga Arfa.

 Fili tarwal babu tanti babu dakunan kwana. A nan ne duk girman mukaminka z aka gane daidai kake da sauran bayain Allah masu ibada a wajen. 

 Ana so a kwana a wannan fili sai dai ga tsofaffi da mata da marasa lafiya ne kawai za su iya barin wajen cikin dare. 

A filin Muzdalifa ne aka dibar duwatsun da za a jefi shaidan da su washegari. 

Lallai dole wannan kwana mai matukar muhimmanci da ke kara wa mutum yakana da tsoron Allah ya kasance wani abin kewa a zuciyar maniyyata na bana.

 3.Jifan Shaidan Da an yi sallar Asuba sai a kama hanyar tafiya Jamrah, wato wajen da za a jefi shaidan. Mafi yawan mutane kan tafi ne da kafa daga Muzdalifa duk da nisan da ke tsakanin wuraren biyu. 

Amma da yake abu ne na bautar Allah ba lallai ka gane irin nisan tafiyar da ka yi ba ma. A kan samu turmutsutsu a wasu lokutan amma hukumomin kasar na aikin fadada wajen kusan duk shekara wanda hakan ke rage cunkoso. 

 

Sannan ga wasu naúrori da ke fesawa mutane ruwa tun a kan hanya don rage musu tsananin zafin da ake ji. Wayyo ko ni ma a yanzu da nake rubutun nan na ji kewar wannan aiki mai dumbin lada duk da cewa duk a hajjina ta farko har suma nay i a wajen, a ta biyun kuwa faduwa nay i abn sum aba amma na fita hayyacina. Ana shafe kwana uku zuwa hudu wajen zuwa jifan shaidan.

Mina

 4.Zaman Mina A ranar 8 ga watan Zul Hijjah ne ake fita Mina don fara ainihin aikin Hajjin. Gaskiya rayuwar zaman Mina na kwanaki hudu na ciki da dumbin aikin lada da kuma koyon darasi na rayuwar duniya. 

Daga cikin abubuwan da za a yi kewa dangane da wannan waje akwai ayyukan ibada da suka hada da zikirai da nafilfilu da sallolin jamí da karatun kuráni da zuwa jifan na tsawon kwanin da za a yi a wajen Mina ne wajen da ake haduwa da mutane ta yadda ba lallai ka hadu da wadanda ka sani a Makka ko Madina ba amma Minat ta zama tamkar mahada Ina kewar zaman Mina kuma na san dukkan maniyyata na bana ma na kewar wajen. 

5.Dawafi Farin gani ido da ido da Kaába sai a Dawafi. Dawafi ana fara yin sa ne da zarar an shiga birnin Makkah ba sai an fita Mina ba. 

Ana fara yin dawafin Umara, sannan akwai dawafin ranar Sallah da ake kira Dawafil Ifada, sai kuma dawafin bankwana bayan an kammala aikin Hajji a lokacin da mahajjata za su koma garuruwansu. Lallai dole ma mahajjata su yi kewar dawafi saboda irin shaukin da ke cikinsa. 

Ga ka ga Dakin Allah, me ya fi wannan dadi. Ga irina mai raunin zuciya kuka na kan yi idan ina dawafi, don ji na ke babu wani shamaki tsakanina da Mahaliccina a badini.

 6.Saáyi ko Safa da Marwa Safa da Marwa ibada ce da ke tafe hannu da hannu da dawafi, don idan aka yi dawafan nan in dai ban a nafila ba sai an biyo bayansu da Saáyi. Safa da Marwa ibada ce da ake tafiya ana gabatar da adduóí a cikinta. 

Sannan za ta dinga sa ka tsoron Allah da tunanin haka Nana Hajara matar Annabi Ibrahim AS ta dinga yi lokacin da take nemar wa jaririnta Annabi Ismaíl ruwa don ya sha. Lallai wannan ibada dole maniyyata su yi kewarta. Abubuwa biyar da suka kamata a sani game da Ranar ArafatHajj 2021:

 Sharuɗa takwas da Sudiyya ta gindaya kan hajjin bana

 7.Madina Masallacin Manzon Allah SAW ”Yaushe za mu Madina ýan uwa, zuciyata ta ki dangana ga idanu na zubar ruwa, yaushe za mu ziyara dausayin sabunta shakuwa….,” in ji wani mawaki mai suna Hafiz Abdullah. Lallai kam zuwa ziyara Madina ka samu kanka a Msallacin Maznon Allah SAW babban alámari ne mai tsayawa a rai. Shiga Rauda da ganin Mumbari da ganin Kabarin Manzon Allah SAW, lallai wadannan manyan alámura ne masu tsayawa a rai. Dole maniyyata su yi kewar wannan lamari.

 Daga nan kuma alhazai za su karasa wajen Makabartar Bakiá inda mafi yawan sahababi da matan MAnzon Allah SAW ke kwance don ziyara. 

8.Uhudu Ziyara zuwa Dutsen Uhudu na daya daga cikin abubuwan da za su dinga tsayawa maniyyatan da ba su samu zuwa hajji ba a bana. A nan ne za a zagaya da alhazai don su ga baurburan sahabban Manzon Allah da aka kashe a Yakin Uhudu.

 9.Masallacin Quba Ziyara zuwa masallaci na farko da Manzon Allah SAW ya fara yin sallaha a cikinsa loakcn da iya isa Madina yayin hijirarsa. A kan yi sallah rakaá biyu a yi adduói sannan a koma cikin Madina. Gaskiya zuwa Quba ma abu ne mai dadi da tsayawa a rai. 

10.Mikati Idan daga Madina ka fito za ka tafi Makkah don fara ibadar aikin Hajji to mikatinka yana Zul Hulaifa ne. Idan daga Jeddah ne kuwa to a nan din z aka dauki mikatin haramar Umara ko na Hajji da Umarar, ya danganta da irin hajjin da za ka yi. Ba abin da na fi tunawa irin wankan daukar niyya da ake yi a buga layi a gaban bandakunan, na mza daban na mata daban. Idan an fito wanka sai a saka ihrami a shiga mota a fara talbiyya ana ”Labbaikallahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik…,” har sai an shiga Makkah.

 11.Tafiyar mota Wata makaranta ce mai zaman kanta da za a yi kewa. Ko dai daga Makkah zuwa Madina ko daga Madina zuwa Makkah ku kuma daga Jiddah zuwa Makka ko Madina ya danganta da yadda tsarin tafiyarka ya kasance. Amma dai idan ana wucewar nan z aka yi ta rayawa a ranka ko nan wajen yaya yake a zamanin Annabi SAW? Sannan a kan tsaya a kananan garuruwa don yin sallah da cin abinci, abin dai gwanin dadi.

 12.Ruwan zamzam da dabino Duk da cewa a yanzu haka a kowace kasa idan kana so za ka iya sayen zamzam da dabino, amma ba dai kamar a ce kana gindin maganin ba, inda famfo kawai za ka bude a cikin Masallacin Harami ka sha iya shanka.

A Madina ma ga shi nan an zuba a tuluna na zamani a sha a koshi. Dabino kuwa ai ko ba komai zaka yi tsarabar Ajwa mai yawa daga Madina.

 13.Sayayya Bayan aiyyukan ibadah alhazai kan kasha kwarkwatar idanuwansu ta hanyar shiga shaguna don sayen tsarabobin da za su kai wa ýan uwa da abokan arziki. Kaya ne iya dibarka dole kar bar saura a inda ka gan su. Da wahala ka shiga lungu ko sakon da ba z aka ga shaguna ba. Sannan ga rukunin shaguna na zamani a cikin manyan otel-otel din da ke daf da Harami inda ko b aka sai komai ba dole a bai wa ido hakkinsa. Watakila bana da na je da na sayo kallo-kallo.

 14.Shinkafa kaza da tuwon takari Allah Ya bar mana shinkafa kaza. A gaskiya na san mafi yawan maniyyata na bana za su yi kewar cin shinkafar nan da ake juye ta a leda a dira mata bankararriyar kaza a matsa mata lemon tsami. Wayyo, garin dadi na nesa. Sai dai wasu alhazan duk da dadi irin na shinkafa kaza su sun fi son cin abincin mutanenmu mazauna can irin su tuwo da sauran su. Amma ni dai Allah na gani na fi son cimar Larabawa. 

15.Laban Garin dadi na nesa. Duk da cewa akwai yogot kamar yadda aka fi sanin Laban da shi a kasashenmu, to gaskiya na Saudiyya daban yake. Na san ban i kadai ce zany i kewar Laban ba muna da yawa. 

16.Karbar sabil Bar batun girman mukami ko matsayi, a wasu lokutan dole ka samu kanka a karbar sabil Kai ni kam ma dai ina da shaáwar karbar sabil dinnan don kuwa kayan dadi ne masu kudin Larabawa ke cika leda da su ana rarrabawa bayin Allah da sunan sadaka. Ba dai na shiga rububin karba amma da an ba ni nake amshewa ina Allah Ya karba. Bana kam na san ba masu karbar ba kawai su ma masu rabawar sai sun yi kewar rashin rabawa da yawa. 

17.Mu hadu a gaban Darut Tauhid Kalmar mafi yawan mutane kenan idan suna son yin mahada da ýan uwa ko abokansu a bakin Masallacin harami. Gaban katafaren otek din Darut Tauhid ya zama matattara dumbin mutane a lokacin aikin Hajji. Da Allah Ya yi zuwanmu a bana da sai dai na yi wa abokan aikina Baraátu ko Umaymah da muka yi niyya tare waya na ce to mu hade a gaban Darut Tauhid bayan Sallar Laásar.

 Daga nan sai mu wuce KFC cin kaza da dankali. Watakila na manta ban sanya wasu abubuwan da maniyyata za su yi kewa ba, amma dai na san na tabo muhimman da kowa zai iya yarda da ni cewa sun isa saka mana kewar wannan ibada mai dadi da dumbin lada.

                           يوم أعرف مباشرة

Allah Ya sa muna da rabon zuwa badi. 

ALLAH KARBI IBADINMU KABAMU DACEWA DUNIYA DA LAHIRA AMIN.

Leave a Reply

Back to top button