Shugaban hukumar jarrabawar NECO (National Examination Council) professor Ibrahim Wushishi ya sanar da cewar dalibai miliyan daya da dubu dari uku ne suka zauna jarrabawar SSCE (Senior Secondary School Examination) a duka fadin kasar nan a inda yace za’a saki sakamakon a tsahon sati uku kacal.
Shugaban ya sanar da hakanne a lokacin hira da manema labarai a babban birnin Yola dake Adamawa cewar dazarar an kammala jarrabawar hukumar zata fara maka ta domin ganin sun cimma alkawarin da sukayi. Professor Wushishi yace a tsahon sati biyu zuwa uku (3rd September 2021) zasu kammala maka jarrabawar.
Babban jami’in ya kara da cewar sun shirya tsaf domin fara gwada jarrabawar Objective a sabon jadawalinnan na Examination computer Based a inda hukumar zata kara karkade matsalar nan ta magudin jarrabawa.