CRYPTOCURRENCY

DALILAN DA YASA Pi NETWORK ZAI KAI $100 A CEWAR WASU MASANA.

Sponsored Links

 

Pi Network: Pi Liquidity ✍️

Bari nayi magana kadan game da tattaunawar da ake yi cewa yaya za’a yi Pi Network su samu kudin da zasu saka a matsayin Liquidity ma Pi yayin da za’a yi launching dinsa a Mainnet, wannan wata babbar magana ce, kuma itace abinda masana suke ta tattaunawa.

Maganar da ake yi itace idan za’a zuba Liquidity na kudi ma Pi Network kuma yazo ya bayyana a Dollar dari (100 US Dollars) da ake zato, dole sai an saka masa aqalla Dollar Trillion biyar.

Saboda yawan Total supply na Pi da kuma yawan Miners dinsa, wanda a yanzu (29-09-2021) Litinin, ake da sama da mutane miliyan 25.

Wanda kasuwar Crypto kaf dinta bata kai ko Dollar Trillion biyu ba a yanzu haka.

Liquidity shine babban batu, amma Pi Core Team sun bayyana wasu abubuwan dake bayyana cewa ba kudi za’a zuba ma Pi Network ba.

Domin Pi Network yazo ne domin ya canja tafiyar Crypto Currency a duniya gaba daya, wani abu da ake ce ma (Value Creation) za’a yi, abin da ake nufi da Value Creation shine shi kansa Pi Network ne za’a nema masa matsayin kudi ba tare da kudi ya tallafe shi ba.

Babbar matsalar kasuwar Crypto itace kudi, so, Pi Network suna so su bashi Value dinsa ne, idan kaje ka tambayi masana tattalin arziki zasu fada maka cewa Value Creation abu ne mai wahala, musamman Value Creation din mayar da wani abinda ba kudi ba ya koma kudi.

Farashin Pi Network ya danganci amincewar kamfanoni da manyan cibiyoyi a duniya da Pi Network zai shiga, hatta gwamnatocin kasashe.

Dan haka samar da Monetary Value ma Pi shine babban sauyi mafi girma da duniya ta gani a fannin kudi cikin shekaru dari da suka wuce, ko ma sama da haka.

Domin Crypto Currency acikin BlockChain Technology Kamar wani bangare ne guda daya cikin dubu daga BlockChain Technology, batun kudin Crypto Currency ma a block chain dan karamin abu ne.

Dan haka shi Pi Network, Ecosystem ne guda ake ginawa (Wata duniya ce ta daban a hada hadar kudi da ake ginawa yanzu).

Domin idan aka ce wai kudi za’a zuba ma Pi Network toh cikin minti daya da laughing ana iya dumping kudin gaba daya a lalata Pi din, saboda yawan wadanda suke jira su sauke kudin.

Wani abu da ake ta ganin Pi Network zai yi shine zai shafe labarin tafiyar Bitcoin da ‘kanin sa Etherium.

Ana kyautata zato hatta su ma zasu amince ka bayar da Pi a baka Bitcoin, wanda idan kana son kudi Sai ka siyar dashi.

Pi yazo da Use case din da a yanzu sun fi dubu goma.

A wani bangaren kuma, idan ka lura zaka ga cewa kasar China da Japan sune kan gaba a tafiyar Pi Network, toh amma sai gashi China ta hana harkokin Crypto Currency a kasar ta, menene sirrin.

Sirrin shine China tana nufin ta karya Bitcoin gaba dayan sa, ta kaishi kasa tayi raga raga dashi acikin shirin ta na sharan fage ma zuwan Pi Network.

Me yasa China ta hana Crypto amma kuma a cikin kasar ta ake manyan tarukan Pi Network?

.

Ku duba maganar da Justin Sun yayi, wanene Justin Sun?

Shine mai kamfanin Tron, da Just da Jult Swap, Justin Sun dan shekaru 30, shine mai Coin din BTT, WIN, da Sun Coin, ga uwa uba Tron.

Yace “ku kyale su, karya ne, China tana son Crypto Currency sosai”.

Su Justin Sun sune Crypton duniya, haka idan ka duba maganar da Vitalik yayi, waye Vitalik?

Matashi ‘dan shekara 28 wanda ya kirkiro Etherium, mai kamfanin UniSwap.

.

Yace “Su zasu zo su karbe kasuwar Crypton”, yana nufin China, saboda yasan me ake shiryawa a kasa.

Yanzu haka maganar da ake acikin  (Nodes) da ake dasu a duniya a block chain kasar China tana da kusan guda dubu goma, sai Vietnam, ba a maganar America ko Ingila ma, yanzu haka akwai 14 thousands Nodes akan Pi Network.

.

So, ta yaya mutanen nan ba zasu iya bashi Economic value ba, dama kasar Vietnam da China suna shiri sosai.

Sannan kaje ka duba kaga irin aikin da aka yi akan Pi Network a Hackathon nasu, sai ka rike baki kawai, dan haka bayar da Economic value ma Pi Network kusan zaka ce an gama, domin a Vietnam ma da Singapore suna hada hada da Pi akan Dala dari kowane daya.

.

So, in recent in sha Allah Pi zai zama of Economic value a duniya gaba daya, zuwa December this year.

Dama ai wadannan kudaden takardar da muke amfani dasu (Fiat currency) asalin su ba kudi bane, takardu ne, kudi sune Azurfa da Zinare.

Tafiya ce tayi tafiya a duniya har aka samar da kudin takarda aka musu Value Creation, suka zama suna da Economic value, so haka tafiyar tazo a yanzu akan Pi Network.

.

Yanzu Pi ba kudi bane, amma idan aka samar masa da value din shike nan, kamar yadda ada babu wanda ya yarda da kudin takarda, daga baya ne aka samar masa da matsayin Azurfa da Zinare, shiyasa idan kaje kana bincike karatuttukan Malam Abubakar Gumi zaka ji wani wurin da yake cewa ai wadannan takardun (Naira Notes) ba kudi bane, kwata kwata ba kudi bane.

.

Za kayi mamaki ace wannan dubu dayan dake Aljihun ka ba kudi bane, eh haka ne, kudi sune Azurfa da Zinare, zamani ne ya kawo aka yarda da takarda ta zamo kudi.

So haka tafiyar take akan Pi.

Zan tsaya a nan amma akwai wasu batutuwa da zan tattauna mana su a rubutu na gaba akan Pi Network in sha Allah.   ga Wanda bayyi register ba zai iya anfani da link dina Domin yi a yanuzu  kada kamanta AuwaluNcbn Shine Code Dina.

✍️ AuwaluNcbn. 

Leave a Reply

Back to top button