TASKAR TARIHIN HAUSAWA DA AL'ADUNSU

{ASALI HAUSA DA GINUWAR DAIDAITACIYAR HAUSA DA KA’IDOJINTA}.KASHI NA BIYU BY MZS.

Sponsored Links

kashi na biyu
 Daga wannan lokaci ne aka tabbatar da samuwar Daitattaciyar Hausa da ka’idojin rubutun Hausa. 
Dukkan abubuwan da suka faru a baya za a ga daidaikun mutane ne ke yi da kulawar hukuma, sai dai hukuar ba ta sa baki ba sosai da sosai sai a shekarar 1955 da aka kafa Hukumar Kula Da Lamurran Hausa, wadda hukuma ce da ta yi kokarin daidaita Hausa da samar da ka’idojin 
rubuta Hausar. 
 Ta yi abubuwa da dama, ita ce ta gyara da tantance duk wadansu kalmomin aro da na kimiyya da fasaha. 
 Wannan hukuma ce kuma ta waiwayi aikin da Hans Vischer ya yi a 1952 domin daidaita tunani da zamani, ta samar da kundin da ta kira Rules for Hausa Orthography a 1958. 
A daidai wannan lokaci ne aka tsayar da karin Hausar Kano a matsayin Daidaitacciyar Hausa, sai dai an shelanta cewa duk inda aka sami kalmomi da a cikin garin Kano kadai ake furta su, ana iya maye gurbinsu da wadansu daga kare-karen Hausa can daban da suka fi karbuwa. 
 Bayan da Turawan mulkin mallaka suka bar kasar Hausa, an yi ta kokari daga ‘yan gida a daidaita rubutun Hausa.
 Taro na farko da aka yi shi ne a birnin Bamako na kasar Mali a shekarar 1966, karkashin jagorancin Hukumar UNESCO, inda aka tattauna yadda za a daidaita rubutun Hausa a Yammacin Afrirka.
 A wannan taron ne aka amince a rubuta Hausa kamar haka. 
Haruffa masu lankwasa /b/ da /k/ da /d/ kamar yadda suke yanzu. 
Aka samar da tagwayen haruffa /sh/ da /ts/ da / 
gy/ da /ky/ da /ky/ da /gw/ da /kw/ 
A kuma raba /su/da /na/ wato /su na/ ko /ka na/ 
ko /ki na/ da /ya na/ dss 
A shekarar 1970 kuma an yi wani taron a jami’ar Ahmadu Bello, Zaria inda aka sake kallon aikin da Hukumar Kula Da Lamurran Hausa ta yi a 1958, aka 
samar da sababbin bayanai kamar haka: 
A dinga rubuta /ko’ina/ ba /ko ina/ ba 
Haka a rubuta /yake/ ba /ya ke/ ba, ko /yakan/ 
ba /ya kan/ ba, /suna/ ba /su na/ ba. Da kuma /mutum/ ba /mutun/ ba 
Da /malam/ ba /malan/ ba 
/Ranar kasuwa/ ba /ranak kasuwa/ ba.
 A shekarar 1972 kuma an sake gudanar da wani taro a jami’ar Bayero Kano, wanda shi ma ya yi kokarin daidaita ka’idojin rubutun Hausa, an amince da ‘yan gyare-gyare da dama, wadanda za iya cewa su ne har yau ake amfani da su a duk fadin duniyar Hausa. 
 Ga kadan daga abubuwan da aka amince da su a wurin taron, kamar yadda M.K.M.Galadanci ya 
kattaba.
 Universal nouns are written as one word 
/komai/ ba /ko mai/ ba 
/kowa/ ba /ko wa/ ba 
/koyaushe/ ba /ko yaushe/ ba 
Where the pre-verbal pronoun precedes the tense 
marker it is written as one word. /yakan/ ba /ya kan/ ba 
/yana/ ba /ya na/ ba 
Where the tense marker precedes the pre-verbal 
pronoun it is written separately. 
/za mu/ ba /zamu/ 
/za su/ ba /zasu/ ba A short possessive is joined to the preceding 
nominal 
/dokina/ ba /doki na/ ba 
/rigarsa/ ba /rigar sa/ ba 
/zanenta/ ba /zanen ta/ ba 
But the long possessive is written separately /wani doki nawa/ ba 
/wani dokinawa/ ba 
/wata riga tawa/ ba /wata rigatawa/ ba 
/wani zane nata/ ba /wani zanenata/ ba 
The pronoun object is written separately 
/ya ba ni/ ba /ya bani/ ba 
/mun sa shi/ ba /mun sashi/ ba /ana kiran ka/ ba /ana kiranka/ ba 
Haka kuma an jaddada cewa /saboda/ da / 
watakila/ kalmomi ne a cure wuri guda, ba a 
rubuta su a ware ba, wato /sabo da/ ko /wata kila/ 
ba da sauran su. 
 Taron karshe da aka yi na daidaita rubutun Hausa shi ne wanda aka yi a 
Niamey, a kasar Nijar a 
shekarar 1980, karkashin jagorancin Kungiyar Hada Kan Afirka, (OAU). 
Place the ad code on articles you want ads to appear, in
An shirya wannan taro ne don a mayar da hankali wajen daidaita rubutun Hausa a Nijeriya da Nijar, shi ma wannan taro ya amince da muhimman bayanai da suka hada da: An tabbatar da gajerun wasullan Hausa: i,e,a,o,u 
An tabbatar da dogayen wasullan Hausa: 
ii,ee,aa,oo,uu 
Da kuma bakaken Hausa kusa 33 
Daga lokacin da aka kashe Hausa Language Board 
(Hukumar Kula Da Lamurran Hausa) da aka kafa a 1958 sai aka mayar da 
yawancin ayyukanta ga Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya da ke karkashin Jami’ar Bayero, Kano, ita ce mai kula da ka’idoji da daidaita rubutun Hausa, kuma tun daga 1982 ta yi iyakacin kokarinta na yin wannan aiki tukuru.
  Ita ce ke shirya tarurrukan inganta harsunan Nijeriya (musamman na Hausa da Fulfulde da Kanuri), ta 
kuma samar da aikin fassara kalmomin zamani zuwa Hausa da kuma Kamusun Hausa da ta buga a 
shekarar 2007, bayan sama da shekara 30 ana bincike da nazari da bita. 
 Inda muke ke nan yanzu, ba wani taro kuma da aka kara yi har zuwa yau 
da na sani domin daidaita ko sake shata ka’idojin rubutun Hausa, wanda da zarar an samu wannan dama duk wata matsala a nan za a tattauna ta, a kuma samar da matsaya domin amfanin sauran al’umma. 
Allah
shi
ne masani!

Leave a Reply

Back to top button