SOYYAYYA

Yan Mata Da Yawa Na Rasa Mijin Aure Da Wuri Ne Saboda Wasu Dalilai:

Sponsored Links

 

Yan Mata Da Yawa Na Rasa Mijin Aure Da Wuri Ne Saboda Wasu Dalilai:

A wannan karon zan yi bayani ne a kan wasu dalilai dake hana wasu ‘yan mata samun mijin aure da wuri.

 Bayani na hakika ya tabbatar da cewa, sau da yawa wasu ‘yan matan kan fada cikin larurar rashin samun abokin zama sakamakon girman kai, wanda masu hikima kan ce rawanin tsiya.

 Duk wanda ke wulakanta jama’a, to zai ga iyakarsa. 

Da yawan ‘yan mata yayin da suka kai wani mataki na girma kuma tauraruwarsu na haskawa a wannan lokacin wanda hakan ne yake sa wa samari su yi tururruwar zuwa wajen budurwa don zama masoyinta na aure da na nishadi ma.

 A wannan lokaci ne budurwar ke ganin ta zama tauraruwa wadda hakan ya kan sa ta girman kai wajen zabar masoyi na kwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakanisa ga Allah. 

‘Yan matan su kan zabi masoyi yayin da suka sami wanda ya fi shi, su kan canja akalarsu kan wanda idanuwansu ya gano, haka za su yi ta canzawa har su rasa wanda za su zaba.

 Girman kai da rudin duniya ya kan sa idanuwansu su rufe wa su rasa gane ina suka dosa.

 Ba wani abu ba ne yake janyo hakan illa son rai da kuma son abin duniya shi yake kawo hakan wani lokacin ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu. 

Da yawa a yanzu su kan dauki buri mai girma su dorawa kansu wanda hakan ko kusa ba zai samu ba, idan kuwa ya samu, to z a sha wuya kafin a same shi da sauki karshe a sha wahala.

 Da yawa daga wasu ‘yan mata kan saka wa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan saurayi kamar zubin Fulani irin saurayin da ake ba su labari cikin littafin Hausa za su aura.

 Sai budurwa ta saka wa zuciyarta lallai sai irin wannan namijin za ta aura wanda yake mara makusa kamar shi ya yi kansa, za a samu, amma kafin a samu za a dade a ce an samu wanda ya hada komai ba shi da wata makusa kamar yadda na cikin littafin Hausa yake. 

A Haka kuma wasu kan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so, saboda sun ruga sun bar wa zuciyarsu wannan tsarin. Ko kuma mace ta kudurce cewa, lallai sai mai kudi saboda mijin kawarta ko saurayin kawarta mai kudi ne, don haka ita ma sai mai kudi ko kuma ajinta ya wuce ta auri talaka ko wanda sana‘arsa ba mai girma ba ce, irin wadda duniya za ta san da zaman sa ba.

 Iri-irin wadannan da ma wasu ra’ayoyin nasu wanda ban ambato su ba, to ya kan saka wasu matan girman kai don ba duka ne aka taru aka zama daya ba, sai an amince wa saurayi ringidi- ringidi da zarar wanda ya fi shi ya zo sai zance ya sha bamban. Mata sai ku mun hakuri domin yau rubutun nawa naku ne, ki sani cewa yayin da kika tsaya nuna girman kai za a kai ki a baro komai kyanki. 

Mata su kan rasa na zaba har lokacin da samarin za su daina zuwa, lokacin mace ta huce wannan matakin da tauraruwarta ke haskawa sai kuma ta dawo tana lissafa adadin samarin da ta yi ta na da ta sani tun a wancen lokacin ta zaba daya da ya fi mata a yanzu gashi tana zaune ana aurar da kannenta ta na gani. 

A cikin hali girman kai wasu su kan kudurci su ba za su auri mai mata ba, wani sa in ma har iyaye su kan ba wa yaran gudunmuwa wajen haifar da ruwan idon, yayin da aka rasa wanda za a zaben, sai a dawo ana addu’ar Allah ya kawo koda me mata uku ne, saboda burinsu a lokacin a aurar kar masu zuwa unguwa su rinka ci gaba da zagi ko kuma saka ido a kowanne motsi na yarinyar. 

A cewar wasu ‘yan matan zama da sautayi daya tsautsayi ne, gwara su raba kafa har Allah ya sa a dace, sai dai kuma abin takaicin shi ne, za ku ga wasu mazan na arziki wadanda suke da niyyar yin aure kuma sun je wajen yarinya da zuciya daya, amma ita sai ta ki amincewa da soyayyarsa koda kuwa ba shi da wata makusa a tare da shi ta biye wa samari matasa wadanda ba su da niyyar yin aure a wannan lokacin wato maza ‘yan tayin hira su rude ta su janye zuciyarta da wasu abubuwa wadanda ita a lokacin ba za ta san hakan ba sai ranar da ta yi hankali ko lokacin da na saninta ya zo. 

Ina kira ga masoya musamman mata tun da batuna gare ku nake a yau da ku daina girman kai ku tsaya ku kula wajen zabar miji nagari, don gudun dana sani wata rana. 

Wasu mazan su kan zo wa ‘yan mata da abubuwa daban-daban dan janye zuciyarta, wanda a bayan auren mace za ta ga ba hakan yake ba, sai kuma ta yi da ta sani wane ta zaba, sai a lokacin za ta rinka hango halayyar wancen wanda ta bari ta yi da ta sani ta dauke shi da na sani dai keya ce.

 Wata ma garin girman kai ta zabo wa kanta wanda kullum zai rinka jibgarta ko kuma wanda zai rinka hanata abinci, ya kamata dai ku kula. 

Allah ya sa mudace, amin

Post By Muhiebert Abdullahi

Leave a Reply

Back to top button