Header Ads Widget

Ɗaurin Shekara ɗaya da tarar kuɗi ₦200,000.00 sune Hukuncin duk wanda ya yaudari wata Budurwa.

  


Ɗaurin Shekara ɗaya da tarar kuɗi ₦200,000.00 sune Hukuncin duk wanda ya yaudari wata Budurwa A Kasar Nan. 

_________________   ___________________


Me ake nufi da Yaudara ?

Yaudara shine mutum ya nuna wata manufa ko siffa a zahiri wanda ba ita ce a zuciyar shi ba domin biyan wata buƙatar shi wanda hakan ka iya cutar da wanda aka yiwa, ko kuma, Yaudara itace: “Nuna soyayya ga samari fiye da ɗaya, tare da nuna ma kowanne saurayin cewa auren shi za kiyi.

Don haka, Yaudara wani daɗaɗɗen laifi ne tun a tarihin duniya, zamu tabbatar da haka ne idan muka koma muka bibiyi littafan Tarihi.


Yaudara wata aba ce mai matuƙar tasiri a cikin tunane, walwala da jin daɗin rayuwar ɗan Adam, shiyasa lokuta da dama za kuga idan aka yaudari mace to hakan yakan sanya taji ta tsani aure, ta tsani soyayya kana kuma ta tsani duk wani Namiji inda zata riƙa yimasu kallon azzalumai marasa imani da tausayi, ta riƙa kallon aure ko soyayya a matsayin wani abu marar amfani a rayuwar ta face kawai ya bautar da tunanen ta, hankalin ta ƙwaƙwalwar ta dama gangar jikin ta, to daganan kuma sai ta fara ɗauko ideology na Feminism, Shiyasa ni a ra'ayi na idan kaga mace ta tsani maza, ko aure ko soyayya, to kafin ka fara zargin ta yana da kyau Kaji dalilin ta na yin hakan, wataƙila ka bata uzuri.


Mata da yawa sukan ɗaura alhakin yaudarar akan maza, haka suma mazan, to saidai Ni a nawa ra'ayin dogaro da wasu bayanai dana tattara daga cikin wani Group a Facebook mai suna “Home of Solace” shine: Tabbas Mata sune suka fi yaudarar Maza a Soyayya, domin a Shafin na “Home of Solace” anyi wani Posting da yake cewa: kowa ya faɗi kalma

ɗaya tak akan tsohon masoyin shi, dana tattara duka Comments ɗin da Mata suka yi a ƙasan wannan Posting ɗin sai naga kashi 90 cikin 100 na matan fatar Alkhairi suke yiwa tsofaffin samarin su, kazalika, dana tattara Comments ɗin da maza su kuma suka yi, sai naga kusan Kashi 90 cikin 100 na Mazan zagi da tofin Allah tsine suke yiwa tsofaffin ‘yan Matan nasu, wanda hakan yake nuna cewa mata sunfi maza YAUDARA kenan. 


Amma idan ka kalli abun, sai kaga kamar maza sun fi mata yaudara kuma ba haka bane, dalilin da yasa ake ganin hakan, shine: Su maza suna da ƙarfin zuciya, Juriya da dakewa a duk lokacin da Mace ta yaudare su, amma su kuma mata ba

suda wannan ƙarfin zuciyar ko juriyar a duk lokacin da maza suka yaudare su, to shiyasa sai a riƙa ganin kamar anfi yaudarar su, alhali kuma sune sukafi yaudarar.


MENENE HUKUNCIN YAUDARAR SOYAYYA A DOKAR ƘASA ?


Yaudara a soyayya babban laifi ne a dokar ƙasa kamar yadda VAPPA, 2015 ya bayyana don kuwa yaudara a soyayya yana haifar da Emotional and Psychological Pain (bansan ya Zan faɗe shi da Hausa ba) to kuma dokar ƙasa ta haramta ka haifar ma mutum da waɗannan damuwoyin babu gaira-babu- dalili.


Akwai bambanci tsakanin Breach of Promise to Marry (Saɓa alƙawarin aure) da kuma Yaudara a Soyayya, a cikin wani rubutu na nayi bayanin hukuncin saɓa alƙawarin aure, shiga nan domin ka karanta. 


Sashi na 14(1) na Violence Against Person's Prohibition Act, 2015 ya bayyana Hukuncin ɗaurin Shekara ɗaya ko tarar Kuɗi dubu ɗari biyu (₦200,000.00) ko kuma duka biyun, ga duk wanda ya haifar maka da Emotional ko Physiological Pain,

wanda kuma duka mun yarda Soyayya ita ce abu ta farko kuma Ummul-haba'isin da take haifar da waɗannan damuwoyin.


Haka ma Section 14, Subsection 3 na VAPPA, 2015 ya tanadar da ɗaurin wata 6 ko tarar Kuɗi Naira dubu ɗari (₦100,000.00) ko kuma duka biyun, ga duk wanda ya taimaka ko ya bada Shawara akan yaudara wacce ta haifar ma mutum Psychological and emotional pain.


Sannan, yana da kyau mu sani, wannan dokar bata aiki a Jihohin: Kano, Katsina, Gombe Zamfara da Lagos.


A ƙarshe, duk wacce ko wanda ya samu wannan matsalar zai iya zuwa babbar kotun Jiha ko ta tarayya domin neman haƙƙin sa.

Posts by Shehu Rahinat Na'Allah

Post a Comment

Previous Post Next Post