Header Ads Widget

Tabbas Jinkirin Aure Jarabawa Ne Ga Wasu Mutanan Wasu Kuma Sabanin Hakan.

 


Tabbas Jinkirin Aure Jarabawa Ne Ga Wasu Mutanan Wasu Kuma Sabanin Hakan. 

 

Duk kusancinka da alaƙarka da mace kar ka tambayeta cewa:


Yaushe za ki yi aure?

• Ba ki yi aure ba har yanzu?


Irin waɗannan tambayoyin, akwai waɗanda saboda da Takaice da ciwo, har kuka suke in sun shiga ɗaki.

 Kai ba zaka gane irin raɗaɗin da suke ji a ransu ba.


Kamar kai ne ka gamu da jarrabawar SPILLOVER a jami'a, shekaru 2 kana zuwa gyara; wani ya tambayeka cewa, 


"ME YA SA HAR YANZU BAKA YI GRADUATION BA?"


AURE a karan-kansa, ba kan kowa ya wajaba ba, matuƙar ba zaka afkawa alfasha ba. 


Akwai waɗanda aure ya zame musu wajibi, wasu mustababbi (abin so), wasu makruhi, wasu ma haramun ne a kansu su yi auren. Wannan ƙa'idar tana hawa kan kowanne jinsi, 'namiji' ko 'mace. 

 [Fiqh Al-Sunnah, 2/15].


AURE BABBAR NASARA CE A RAYUWA, MUSAMMA GA 'YA MACE. 


Amma babu inda addini ya ce, in mace ba ta yi aure ba, ta zama 'wata mai laifi' ko in ta mutu bata yi aure ba zata shiga 'Aljanna' ba. Ba laifi ba ne ina mace ta zauna ba aure, matukar zata kiyaye mutuncinta.


A al'adarmu ake ganin, in mace bata yi aure ba, tamkar wani LAIFI ta aikita, ko a cikin gidaje, a gaban iyayenta, a yi ta tsangwama mata, kullum a cikin takaici.

Akwai Wasu Matan da suke daukar Auren Kamar wani hanun jarine idan ka zu gurin su Da zumar aure. 


Amma Sai ta mai daka kamar wani Asusu na ATM MACHINE Kullum bani bani Har ma nemin auren nata ya fuskanci Ba San Shi take da Gaskiyya Abin Hannun sa take so ba Shi ba Aure. 

Don Haka tazama tana ta bata wa katan Da Kanta lakaci Baza tayi aune ba sai ta girma Sai kuma Azu Ana so Ko wane IRI ne kawai Yazo. 


Wasu Kam Sunfi gane suje Sita is kan cin su A gari har sai ta kare musu sannan su halkanta....... 


Ga wadanda suke da Matsalar Ya kamata Al'umma Su Daina kyarar su Da kuma Ciz gonawa Musu Domin  Haramune A SHARI'A


DAGA Aliyu M. Ahmad

Post a Comment

Previous Post Next Post