YANDA AKE AJIYE LAMBAR WAYA AKAN GMAIL

 


Yanda zaka ajiye lambar wayarka akan gmail


Assalamu alaikum jama'a barkanmu da warhaka adaidai wannan lokacin acikin wani sabon darasi.

Ayau zan nuna mana hanya mai sauƙi wadda zaka bi ka ajiye lambar wayarka akan gmail,sai dai nasan da yawa daga cikin masu biyarmu sun san yanda akeyin to amma wasu kuma suna tambaya saboda haka nace zanyi ɗan ƙaramin bayani akai.

Da farko dai ina fatan kana da gmail akan wayar taka daga kawai sai shiga cikin inda ake rubuta lambar waya sai ka rubuta lambar daga nan zata nuna maka inda zaka ajiye lambar kamar haka 

Phone 

Sd card

SIM

Gmail

To kawai sai ka zaɓi gmail daga shikenan ka gama.

Yanda zaka tabbatar lambar ta hau kan gmail ɗin 

Zakaje ka duba browser ɗin da kake amfani da ita sai ka rubuta www.contact.google.com
Ko kuma ka danna wannan link ɗin kai tsaye zai kaika ka ga adadin lambobin da suke kan gmail ɗin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Technology