YANDA MAHADDATA ALQUR'ANI SUKE YIN RUBUTUN ALQUR'ANI


 YANDA MAHADDATA ALQUR'ANI SUKE YIN RUBUTUN ALQUR'ANI


Assalamu alaikum jama'a barkanmu da ka cewa daku a wannan lokacin. 

A yau zaku jimu da wata hanya da mahaddata Alqur'ani sukeyin amfani da ita wajen rubutun Alqur'ani.


Alqurani dai shine littafin da Allah ya saukarwa annabinmu Muhammad (S.A.W) , littafi mafi Tsarki a duniya gagara badau wanda ba'a iya ƙara masa komai domin ya cika.


Mahaddata Alqur'ani suna fara yin hadda kammalalliya cikakkiya tun daga baƙara zuwa nasi.Wasu suna yin sauka kamar biyu ko uku ko hudu kafin su fara yin satu.

Satu ma'ana bayan mai hadda ya gama yin haddarsa to kafin ya fara ɗaukar takarda yayi rubutun Alqur'ani sai ya ɗauki allo ya fara yin rubutun Alqur'ani a allon amma da ka batare da ya duba takarda ba.Daga nan kuma bayan malamansa sunga baida matsala wajen rubutun da gyara sannan kuma sai karya takarda ya fara ɗaukar takarda yana rubuta Alqur'ani daga farko zuwa karshe.Hanyoyin yin hadda Alqur'ani


 1. Yin rubutu a allo 

 2. Karantawa a littafin

 3. Biyawa ba Alqur'anin

 4. Sauraren karatun(kira'a)

Waɗannan sune hanyoyin da mahaddata suke yin amfani dasu wajen yin haddar.

Amma fa hanya ta farko tafi domin ita zaka rubuta sannan za'a karanta maka kana ganin abinda ake karanta maka iya wurin da ka rubuta shi ake so ka haddato kaga hankalinka zai iya rubutun da allonka.Duka hanyoyin da yawa mutane sun haddace Alqur'ani da kowace hanya daga ciki.


Abubuwan da suke zaunar da haddar Alqur'ani 


 • Yawan yin tilawa

 • Yawan yin taƙara (maraja'a)

 • Yin sallar dare da karatun  inda ka haddace

 • Musaffa

 • Ja dare

 • Addu'a

 • Naci

 • Hakuri 

 • Juriya

 • Kaucewa Saban Allah

Domin ganin cikakken yanda ake rubutun ka kalli wannan videoShawarwari

Yan uwa Alkur'ani shine littafin da babu kamarsa a duniya littafin da ba'a edition ba'a masa update ba'a kara masa komai domin ya cika,saƙon dake ciki ya haɗe tun daga farkon duniya zuwa ƙarshe.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Technology