Yau saura wata ɗaya da kwana shida a kammala Pi Network Hackathon zagaye na biyu (2nd Edition).


 Pi NETWORK Updates:

Yau saura wata ɗaya da kwana shida a kammala Pi Network Hackathon zagaye na biyu (2nd Edition) wadda hukumar Pi network suka buɗe kuma duk wani mutum mai fasahar inventing ɗin wasu keɓantattun abubuwa guda huɗu da Pi Coreteam ɗin suka ware za'ayi hackathon ɗin akan su yake shiga, inda aka buɗe tun daga ranar 09/01/2023 inda za a rufe ranar 28/02/2023.


Ƙafar yaɗa labarai akan harkokin Crypto Currency na C.Z mai Binance (BSC News) sun fitar da bayanan cewa daga farkon fara hackathon ɗin nan zuwa yau an samu dubannin kamfanonin da sukayi ta turereniya wajen shiga wannan program ɗin inda daga ƙarshe aka tantance kamfanoni guda dubu goma sha takwas (18,000) a matsayin waɗanda suka zamo zakaru kuma masu shiga wannan hakathon ɗin.


Ba wai an kammala shiga gasar ta hackathon bane ba, a'a!

Ana shiga har yanzu, duk wani ƙwararre a fannin ƙirƙirar wani abu na kimiyya da fasaha da suke cikin waɗancan abubuwa guda huɗu da aka ware domin yin Pi hackathon ɗin nan akan su to zai iya shiga, sai dai akwai ƙa'ida guda ɗaya zuwa biyu na samun damar shiga wannan program ɗin kafin a tantance mutum kamar haka-:


1). Dole duk basirar ka da ƙwarewar ka a fannin kimiyya da fasaha sai kun haɗa team ɗin a ƙalla mutum huɗu kafin ku samu damar shiga cikin program ɗin harma a tantance ku.


2). Idan baku kai huɗu ba, misali ko ku uku ne ko biyu ko ɗaya, to sai dai ku samu wasu team ɗin ku roƙe su ku shiga cikin su kuyi mergining domin samun damar shiga program ɗin.


A taƙaice dai waɗannan sune primary instruction ɗin da ake so mutum ya cika kafin ya samu damar participating a program ɗin Pi hackathon da yake gudana a halin yanzu.


MENENE PI HACKATHON?

Pi Hackathon-: Wani shiri ne na musamman wanda yake a matsayin utility ga jama'ah da Pi coreteam ta ƙirƙira a matsayin dama ga duk sani mai ilimin ƙirƙirar wani abu na zamani, ko mai wani kamfanin da yake yin wasu aiyuka, ko kuma ga duk wanda yake da wata sana'ar hanu da zai je yai rajista da Pi network a ɓangaren hackathon ɗin domin a ɗauke shi ayi masa gwaji akan wannar sana'ar tashi idan ya haye sai a bashi kyauta na kuɗi masu yawa.


A shekarar 2021 Pi coreteam sun gabatar da Hackathon ɗinsu na farko inda kamfanoni da yawa suka samu shiga aka kuma aiwatar da gasar aka ɗauki kamfanoni guda goma aka basu kyaututtuka kamar haka-:


√• 1st Postion kyautar Pi guda dubu ashirin da kuɗi dala dubu ashirin (π20k with $20k).


√• 2nd Position kyautar Pi guda dubu sha biyar da kuɗi dala dubu sha biyar (π15k with $15k)


Da haka dai ana yin ƙasa ana rage dubu biyar-biyar ta ɓangaren adadin Pi da kuma dalolin da ake bayarwa a matsayin kyauta har aje kan wanda ya fito a na goma Inda shi kuma za a bashi kyautar Pi guda dubu biyu da kuɗi dala dubu biyu (π2k with $2k).

Akan hakan, Pi coreteam ba ƙananan maƙudan kuɗaɗe suka kashe ba wajen wannan Program ɗin.


To bana kuma a wannan shekara ta 2023 shi ne suka ƙara fitar da wannan program ɗin a karo na biyu, inda shi kuma za a bayar da kyaututtuka kamar haka-:


å 1st Position

Za a bashi Pi guda ɗari ɗaya ko kuma a bashi kyautar kuɗi dala dubu talatin (100π or $30, 000), kamar yadda twitter handle na Pii Network News suka tabbatar da haka.


Ku fuskanci maganar nan fa da kyau Pioneers, kyautar fa ita ce-:


√• Za a baka Pi guda ɗari kacal


Ko kuma 


√• A baka kuɗi dala dubu talatin ($30, 000).


Kenan wannan critically yake nuna mana darajar Pi guda ɗari dai-dai yake da dala dubu talati (π100 = $30,000).


Idan ka tafi da lissafin ƙasa har zuwa kan wanda yai na goma, shi kuma kyautar sa ita ce-:

√• Pi guda goma ko kuma kuɗi dala dubu uku (π10 or $3,000).


To idan Pi ɗaya ne fa, dala nawa zai kama kenan?


Bayan an fitar da zakarun da suka fafata a ɓangaren fasaha a duniyar Hackathon na Pi Network, to waɗannan zakarun su zasu kasance ma'aikata ne na dindindin a hukumar Pi Network wajen gudanar da aiyuka wa jama'ar duniya da irin abinda suka ƙware akai, su kuma ana biyan su da Pi network, inda su kuma hukumar Pi network ɗin zasu dinga samun kuɗin shiga sanadiyar wannan aikin da waɗannan hackers ɗin zasu dinga yi ƙarƙashin su.


Pi network Hackathon ya biyo bayan sanarwar da Pi Coreteam suka fitar ne a sabuwar Whitepaper ɗinsu na December 2023 akan MASS KYC da kowa yake dako/tsumayi/jira, ana sa ran cewa da zaran an gama Pi Hackathon ɗin kuma za bayar da Pi Mass Kyc ko kuma a ninninka adadin waɗanda ake baiwa slot ɗin KYC ɗin da kaso goma sha biyu akan yadda ake yi a baya.


Bayan program na Pi hackathon, akwai kuma zuwan ranar nan ta Pi-Day ranar 14/03/2023 idan Allah ya kai mu, inda ake sa ran manyan abubuwa zasu faru a wannan rana, kuma da ga nan babu babban wani abu da zai biyo baya sai "Open MainNet" kamar yadda sanarwar hakan ta gabata bisa tsammani.


Fatan mu dai Allah ya tabbatar mana da dukkan alkhairan dake cikin wannan Project na Pi ɗin.


Ibrahim Ra'ees Abou Mous'ab 

Monday

01/07/1444 H.

23/01/2023 M.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Technology