GIRKE GIRKE

[KOKASAN AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM]…

Sponsored Links

 


WASU DAGA CIKIN AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM


  Kankana uwar ruwa ta nada amfani susai a jikin dan Adam musan man ma a lokacin da ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimaka ma idanu.


  Kankana tana da matukar mahimmacin kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda ‘ya’yanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus da copper. 


    [WASU DAGA CIKIN AMFANIN KANKANA GA JIKIN DAN ADAM]


> Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen maganin cututtuka da dama.


> Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.


> Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan nitric oxide dake kara ma namiji karfin gaba.


> Tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.


> Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan adam.


> Tana da sinadarai masu kara karfin kashi  bone  da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki {joints}.


> Zakin cikinta kuma na ba mutum karfi, tana kuma kara ma jiki ruwa.


> ‘Ya’yan kankana ana amfani dasu wurin magance ciwon diabetes, idan aka tafasa ruwa ‘ya’yan kankana 1litre na tsawon mintina 45, sai a ringa shan ruwan kamar shayi.


> Ya’yan kankana suna taimakawa wurin samun karfin jiki bayan rashin lafiya sannan kuma suna kara kaifin tinani.


.> ‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji.


> Tana haifar da samuwar wadataccen barci.


> kankana na taimaka ma fata saboda sinadarin lycopene dinta.


ALLAH YAKAREMU DA LAFIYA AMEEN.


              

Leave a Reply

Back to top button