Hausa NovelsMai Maganin Mata Hausa Novel

Mai Maganin Mata 21

Sponsored Links

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*MAI MAGANIN MATA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*FREE BOOK FROM 1 TO END*

*Zahra Surbajo*

Bisimillahirrahmanirrahim.

*IN KINSAN A KADUNA KIKE KUMA KE BAZAWARACE MIJINKI YA MUTU KO AURENKINE YA MUTU,KO KE BUDURWACE DA KIKA GIRMA BAKIYI AUREBA DA KIKESO DOGARO DA KANKI,IYA ƘWARYAR BIRNIN KADUNA KAWAI,KUMIN MAGANA A 07044600044*

*ME BUƘATAR COMPLETE DOCUMENT ƊIN SHAAWARSHI NAKE 500 NE KITURO KUƊINKI ABAKI*

*HARIJA CE,sabon littafine dazan yishi akan kuɗi 500 kacal,karku bari abaku labari,yazo da salo na musamman shima meso ze iya turo kuɗinshi yanzu ta acct kawai*

*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*

*07044600044*

 

*21*

“Haba mama ay ba mutunci aciki ace na koma kuma da kaina ni kaɗai bezoba gaskiya nide bazan iyaba”cewar fareeda lokacin da hajiya ta kira ƴarchadi ta sanar da ita buƙatarta na adawo da ita.

“fareeda inaso kigane wani abu guda ɗaya shifa wannan auren baki kafu agidanba wanda ni kuma shi nake miki fata kisamu ki kafu ta haka zaki gagari kowa ciki harda shi kanshi bare wata mahaifiyarshi ki fahimta mana”

Shuru fareeda tayi tana juya abun aranta,daga ƙarshe de ta amince da buƙatar mahaifiyar tata.

50k labeeb ya turawa fareeda koda taga alert ɗin tayi mamaki,amma seta share bata ko kira ko sms tai masa ba.

Gyara na sosai ƴar chadi taiwa ƴartata duk azuwan seta sace zuciyar kowa acikin su.

Koda ƴarchadi tace zata rakata hanata tayi inda tace”mama inaso karki kuma shigowa gidana a yanxu kibari inkama ƙasa da kyau ta yadda intai miki zansashi ya ɗauki mataki,dan bazan jure rashin kunyar datake mikiba”crwar fareeda.

“To Fareeda na Allah tabbatar da alkhairi”cewar ƴar chadi tana rungumota.

Mota drop ta ɗauka har gida,inda ta shige part ɗinta,batare data ko kalli sashin fadeela ba.

Ɓangarenta ta gyara sosai,da sosai,sannan tai wanka da turarukan maganin mallaka da ƴar chadi ta haɗota dasu.

Abinda zataci ta samawa kanta,sannan ta ɗora girkin tarbar megida.

*******

Gidan wani abokinshi sukaje shida fadeela basu dawo gidanba se gab da magriba,inda me gadi yasanar dashi hajiya amarya ta dawo.

Ko kaɗan fadeela bata nuna tajima me akace ba bare ta ɓata ranta

Shiko tsalatu ya shiga,dan besan yazeyi dasuba,tunda fadeela besanar da ita amarya zata dawo ba,duk da ba laifinshi bane tunda shima basu sanar dashiba.

A ɓangaren fadeela yayi wanka yayi sallahyaci abinci amma be cika cikinshi sosai ba,sannan suka koma falo inda rabin hankalinshi nakan fareeda,dan be kyautaba dan yasan taji dawowarshi.

Ƙarfin hali yayi yace”baby ƙanwarkifa ta dawo ɗazu”

Gyara zamanta tayi sannan tace”barkanta da dawowa an barosu lfy ko?”ta faɗi ba tare data kalleshiba bare yaga wani fushi atattare da ita.

 

“Bari inje mu gaisa in na dawo to in kuma saida safe to aymim afuwa,”ya faɗi kamar yaron dake tsoron uwarshi.

Murmushi tayi ta shafo gefen fuskarshi tace”karka wani ji ka damu prince jeka kanka tsaye,Allah tashemu lafiya.kaga yau na huta da sukuwarka”ta faɗi tana shafo dick ɗin.

Dariya yayi ya riƙe hannunta yace “ay zan dawo baby bazan miki da wasa ba kuma”ya faɗi yana kashe mata ido.

Rakoshi tayi har bakin ƙofa,ya rungumeta sannan ya lalubi bakinta ya manna mata kiss,sun jima ahaka kamin ta ƙwace kanta ta koma ciki shi kuma ya wuce yana ɗaga mata hannu.

Da sallamarshi ya tura ƙofar falon ya shiga,inda be ga kowa a cikiba hakanne yasa yabi hanyar dazata kaishi ɗakinta inda can ya sameta kwance kan kujera tana latsa waya,

Da ƙyar ta amsa sallamarsa ya shiga yanemi gefen gado ya zauna,yana kallonta.

Ɗauke kai tayi bata kulashiba ita ala dole fushi take,be bi ta kanta ba,ya miƙe ya fice daga ɗakin ransa na masa zafi danshi bega abinda yay mata da zesa tai fushi dashiba.

Ɗakinshi yawuce yayi alwala yayi sallar ishai,sannan ya sauya kayansa zuwa na bacci yabi lafiyar gadonshi ya kawanta,ya janyo wayarshi ya kira fadeela.

Bata jima tana ringing va ta ɗauka tunkan yace komai ta rigashi da cewa,”prince mantuwa kayine zaa miƙo maka?”

“Ko ɗaya baby pls haw online muyi mgn a whatsapp”yana kaiwa nan ya kashe wayarshi.

Ayko ta hau dan tunaninta wani abunne se kawai yace hira zata tayashi kan yayi bacci.

Bata bincikaba amma ay tasan va lau ba haka ta biye mishi sukai ta hira har wajen ƙarfe biyu na dare.

Shigowar fareeda ɗakinne yasa shi yiwa fadeela voics da cewa “nagode baby da ɗebe kewa,seda safe kikwanta haka”

“To prince mukwana lfy agaida amarya”itama tayo mishi voice ɗin,ya kunna yaji sannan ya kashe ya ajiye wayar, ya ɗago ya dubi fareeda wacce wutar kishi keci a fyskar tata.yace

“baki iya sallama bane?”

Shuru tayi batace komai ba,shima bin ta yayi ido.

Kumude je zuwa.

*bana adding a group dan haka kar atambayeni,in so kike in saki to ki biya 300*

*masu son zama cikin group ɗina suna karanta paid book ɗina,tsawon shekara guda to ku biya 1500 insaku a group ɗin da bazaki sake siyan littafina ba se kin shekara.*

FREE NE HAR ƘARSHE

07044600044

Leave a Reply

Back to top button