Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 18

Sponsored Links

Chapter 18

Zan iya cewa tunda na taso ba taɓa tozartani irin wanda fadila ta mun yau ba,wai shin ina soyayya da mukewa juna yake ina kauna dake tsakanin mu ina aminci da mukewa juwa menama fadila wanda ta zaɓi yamun haka sanin ba mai bani amsa yasani goge hawayena ina mai kokarin tsaida kukanda ke tasomun tun daga ƙasan zuciyata har muka ƙaraso anguwan mu sauƙa nayi nami ƙawa mai napep ɗin kuɗi sai cemun tayi ai wanda ya tsaidashi yabada kuɗin godiya namasa duk da bansan wanda yake cewa yabada kuɗin ba.

Sai da natsaya bakin ƙofan gida kaɗan na daidaita nutsuwata sannan nashiga cikin gida bakina ɗauke da sallama khadija dake alwalan sallar magariba ita ta amsamun sallama danayi”sannu da xuwa anty aisha,
“”Yauwa khady ina mubaraq?”yaje sallah masallaci ta bani amsa.
“Yauwa idan kigama alwalan ɗauki wancan ledar ki miƙashi ga maman salmanu da to amsamun ni kuma na dauki buta alwala nayi nashiga daki na shimfiɗa sallaya na tada sallah.

daga ni har Anna ba wanda yatashi saida mukai sallan isha’i sannan add’oin neman tsari na jima ina addu’an neman sassauci kan abunda nakeji a cikin raina dan zuciyata namun zafi har wani irin turirin zafi nakeji,Kasa cin abincin nayi da zaran nakai abincin bakina sai abunda yafaru dani dazu ya faɗomun daga karshe hakura nayi da na wanke hannu na nakoma gefe na zauna,a tsanake Anna ta dubeni tace”lafiya naga bakici abincin ba?
Ɗan murmushi yake nayi nace”lafiya anna kawai banajin cin abincin ne Allah ya kyauta tace.

Muna cikin hira saiga maman fadila kaman anjehota ko sallama babu kallon ta Anna tayi tace”a’a Rabi kece lale marhabin shigo daga ciki mana…dagawa Anna hannu tayi tace”banason munafinci ai wallahi maman aisha nayi mamaki dama bazaka taɓa sanin masoyinka ba,sai abu yasameka wani irin taimakone bamu muka ba arayuwa haka fadila zata tasani gaba tasa na zubo muku abinci ta dauko ta kawo muku amma saboda baƙin hasada da butulci irin ta ɗan adam shine Aisha zaki rufe ido kiciwa fadila mutunci saboda kawai Allah yarufa mata asiri tasamu aiki mai gwaɓi,to wallahi ahir ɗinku daga ke ha mahaifiyar taki idan ita ke aikoki wallahi wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa.

Banzaye dangin tsiya wayasan asalinku wama yasani ko saida aka gama yawun dandi sannan nitsuwa tazo ma akaxo inda ba ba wanda yasanku kuka ɓoye kanku idan ba haka ba ai duk ɗan halas yasan halacci wallahi,tunda tafara surfa masifa ba wanda yace da ita ci kanki daga ni har Anna sau kukan baƙin ciki daya kubce mun nasan nice silar komai da ke faruwa yanzu,da nayi shiru da bakina da ba wanda ya isa yaciwa mahaifita mutunci haka ba tasan hawa ba bata kuma san sauka ba,anzo har gida ana ci mata mutunci ni kaina mamakin yanda fadila ta iya lauye zancen ta maida lefin kai kawai nake banyi mamakin rashin mutuncin mahaifiyar ta ba,dan kowa dake anguwar nan ya kwana da sanin idan tatashi masifa rufe ido take taciwa kowa mutunci.

Ahmad
Ya kalli ammi da lulun idon sa maikama da wanda yakejin bacci yace”dan Allah ammi kiyi hakuri kinsan ke kaɗaice farin cikin mu…katsesa tayi da cewa”amma ahmad kai baka ganin abunda Alhaji yakeson yi kaman rainane da kuma zubar da mutunci yake neman sayowa kansa,ko so yake mutuncimmu yazube a idon duniya in ba haka ba Ahmad dame Alhaji sunusi yafishi da zaice saide kai ango katare gidan sa gaka ga ɗiyarsa wace irin rayuwar aure zakuyi a gidan ɗaya da surukai ga ɗaki ga ɗaki idan ba dawata manufa aka shirya yin hakan ba.
“Ni de dan Allah ammi kiyi hakuri banaso kusamu tsaɓani da Abba akan wannan magana dan Allah yakare maganan kaman ze saka mata kuka,guntun murmushi da bekai ciki ba tayi tace”shikenan zanyi hakuri amma fa saboda kai bawai dan Alhajin naka da abokin nasa dan sunfi karfina bane ba..da sauri Ahmad yace naji saboda ni Ammi shi duk duniya ba wanda yakeso kaman mahaifiyar sa idan kacire soyayya mahalicci data ma’aiki (s.a.w)to cikon na ukun ammin sane dan ko mahaifinsa saide yabi bayan Ammin sa.
Amma da sharaɗi maganan ammin shi yadawo dashi daga duniyar tunani da yaɗan lula zuba mata ido kawai yayi tace”zaka auri zaɓina ita ka ajita nan ita kuma matar son sai kabita gidan su tunda kunyarda zuciya kare yacinye.
Wani irin zabura Ahmad yayi dan beyi tsammanin jin wannan magana daga bakin Ammin nasa ba,”pls Ammi yace damuwa fal ransa”don pls me ahmad idan kaso nabar wannan magana tasha ruwa ta lafa ba tare da kowa yasan sirrin gidan mu ba to tabbas ka yarda ka amince zaka auri wata matar bayan wanda Alhaji ya zabar maka idan ko bakada ita nice nan zan nemo maka,na baka nan da sati ɗaya kaje kayi tunani kayanke hukunci nima kaina bazan nuna yarda ta da amincewa ta ga Alhaji ba har sai naji hukunci daka yanke akan wannan shin zaka martaba bukatata ko kuwa zakayi fatali da shi.
Take zufa ta karyo masa dan sun sakashi tsaka mai wuya bakuma halin yace yafasa duka dan dukkansu suna da wata hope akansa sannan kuma suɗin iyayensa ne waƴan da sukai sanadin zuwansa duniya bazai iya ƙin yimusu biyayya ba.

Aisha kallon maman fadila tayi da fuskarta shaɓa shaɓa da hawaye tace”dan Allah mama kiyi hakuri in sha Allah daga yau zan dauke idona akan fadila kaman yanda kikace saide kisani banida ƙawa ko yar uwa sama da ita”dallah rufamun baki idan har abunda kike faɗi gaskiyane meyasa….sauri katseta nayi da”naji mama hakan baze sake faruwa ba”dade yafi miki shegiya sai baƙin jini babu mashinshi wama yasa…”ya isa Rabi Anna ta daka mata tsawa tana nuna mata hanyar ƙofa da hannu bawai kinfi kowa iya masifa bane,karkiga idan kin fara masifarki ana shiru ana ƙyaleki bawai tsoronki akeji ba,a’a hauka aka ɗaura miki dan ba mai ganinki da hankali karki sake aibatamun yara dan sufi naki asali inde asaline karkiga kina zaune da mahaifinsu tare kinemi shegenta mun da yara.
Aisha kuma inde nice na haifeta to babu ita babu ɗiyar alheri da kuka mana kuma Allah yabiyaku saide duniyace kubita a sannu watan wataran zakuyi nadama rabi ke saima fita daga cikin gidanki ya gagareki inde irin wannan kuɗin ne.

Maganan Anna da alama ya daki mama Rabi dan koda wasa bata taɓa tsammanin Anna zata iya buɗe baki tayi magana ba saboda irin hakurin ta”baki zakimana maman Aisha aniyarku tabiku keda butulun ƴarki nan ta hau tsalle tana buri kan kace kabo tafara tara mana jama’a abunka da anguwan geto,janta wasu mata sukai sukai waje da ita…

 

ALLAH YASA MUDACE
[5/2, 8:34 AM] Xeenat: 💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

Leave a Reply

Back to top button