Bakar Ayah Hausa NovelHausa Novels

Bakar Ayah 7

Sponsored Links

Page 🖤07🖤

 

_________________________

 

GEMBU babban garine dayake Tsibirin MAMBILA a Sardauna local government dake jihar Taraba a nigeria.
Shine gari na karshe daga nan sai a shiga ƙasar camaroo,hakan nw yasa ya zamo gari mai tarin ƙabilu da kuma tarun yaruka,kama daga irin su Bummi wanda sune manyan ƙabilun garin,sanann kuma akwai Mbubo, Ngebu,Fulani. Wannan sune mafiya yawan mutane da ake samu a yankin,saikuma sauran mutane kaman su Igobo,Hausa,da yaruba,dama wasu daga cikin ƙasar camaroo,wanda mafiyansu kasuwanci ne ke kaisu wajen.
Gembu garine mai tarin ni’ima da kuma ban mamaki.wanda yana ɗaya daga cikin gari mai ƙasar noma ganyen shayi,ba iya ga nigeria ba har ma a africa.
Hakanne yasa wajen yazama mai albarka da kuma tarin hanyoyin samun kuɗi.
Saidai abu dayane yayi wa garin cikas,shine rashin hanyoyin shiga masu kyau,domin nan ma ba iya Nigeria ba,harga duniya baki ɗaya,hanyar garin gembu na ɗaya daga cikin hanya mafi hatsari wajen binta. Saboda manyan manyan tsaunukan da hanyar tabi ta kansu,wanda ake ƙiran su da “Gangirwal” wato a harshen Hausa yana nufin Dutsen mutuwa kenan. Tsaunukane masu matuƙar duhuwa da kuma halittun daji a ciki.
Wannan dalilinne yasa duk da kyawun garin,da kuma albarkarsa baya shiga ran mutane da dama,saboda hatsarin hanyar daza’abi wajen zuwan sa.

Kaɗan kenan daga labarin Gembu,wasu abubuwan zakuji idan muna cikin labari.

___________________

Tun sassafe suke tafiya har rana ta take,kafin suka isa garin Taraba,kasancewar basuda wanda suka sani,hakanne yasasu yanke shawarar kwana kafin gobe su haura mambila,wannan shawarar iyani ce,dan ta fisu sanin wajen.
A super market suka tsaya suka ci abinci,da kuma ɗan hutawa kafin su wuce hotel din da drivern yayi musu booking.
Hajiya zeenah ce takalli iyani wacce take cin abincinta hankali kwance,da alama dama ta saba da irin wannan tafiyar,ba kamar itaba wadda yawanci a jirgi takeyin tafiye tafiye,wannan ma dan tana so ya kasance sirrine shiyasa tayi ta a mota,amma babu laifi tanaji a jikinta kam sosai.
“Wai yanayin hanyoyin basu da dadi bi,gabaɗaya cikina ya hautsine,abicin ma na gagara cinsa da yawa”
“Uhm amma Hajiya inaga kici abinci sannan kuma ki huta sosai,da safema ki karya sosai,don abinda yake gaban mu babban aikine”
“Wane irin aiki kuma,duk wannan jololon drivern ne yaƙi gudu,da yanzu mun haura garin ai,ni na matsu na haɗu da yarinyar nan,naga ya take”
Hajiya zeenah tafaɗa tana yatsina fuska tareda zefah yankan wainar ƙwai a bakinta.
Itadai duk abinda take kallonta kawai take,kallon farko dan zakayiwa Hajiya zeenah kasan batasan wane irin abune yake gabansu ba,a zuwa cikar burinnata.
“Koda yayi gudu ma,bazai yiyu muyi kasadar haura mambila dare yayi mana a wajen ba,saboda hanyar tanada hatsari sosai,inshaaallah saidai gobe mu kama hanya da safe.
Daga haka Hajiya zeenah bata sake cewa komai ba,bayan kaman wasu mintuna ne wayarta tayi ƙara,tana dubawa taga sunan hajiya Ladi.
Kallon iyani tayi wanda itama tagani amma ta ɗauke kai,saboda abinda bai shafeka ba saika bishi da ido.
Da kaman bazata ɗauka ba,saikuma ta ɗauki ƙiran tareda ƙaƙalo murmushin dole tayafa a fuskarta,dan ita kanta tasan idan Hajiya ladi taji abinda yake faruwa,baƙaramin bacin rai zatayi ba,musamman daya zamo so take da tunda tsara komai idan ya danganci auren Jabeer ɗin.
“Hajiya ladi yakk ya kuma yaran?”
“Yara ƙalau,nace dan Allah batun business ɗina ne na dubai,ko zaki shirya ki rakani zuwa jibi,wlh wacce muke tafiya fa itane Yaronta ba lafiya”
“Ahah gaskiya nima bazan samu damar zuwa,dan yanxu haka ma bana gida na tafi ziyara gida,kuma zanyi a ƙallah sati kafin na dawo”
Ɗan jimm Hajiya ladi tayi,kafin kuma sukayi sallama ta ajiye wayar.
“Hmm bazan faɗamiki mai yake faruwa ba harsai na dawo,saboda karma kice baki yarda ba,abinda bazan iya jiba kenan,dan indan akan muradin tarwatsa lubna ne da ahalinta,banajin akwai mai yimin burki”
Duk maganar can ƙasa ƙasa takeyinsa,ita kanta iyani dake gabanta kaɗan kaɗan take jin abinda take faɗa.
Bayan sun isa masauƙinsu nan ma ba kwanciya sukayi ba,duk yanda iyani tayi da Hajiya zeenah ta huta ƙin amincewa tayi,dole saita bata labarin rayuwar garinnasu,wanda rabin tambayar duk akan Rayuwar Bombee ne,
Da safe ƙwanƙwasawar drivern ne ta tashesu,mai suna Iliyah,yaje kawo musu abi karyawa.
Nan ma bayan sunci sun shiryah kafin suka cigaba da tafi.
Kalle kalle suke ta windowa,ganin manya manyan duwatsu,ga kuma yanayin weather daya sanja nan take,yakoma liff liff har a jikin fata.
“Kai iyani amma garinku yana da kyau,wai dama haka yankin taraba yakene? Wanda bai zoba baiyi kallo ba”
“Kallo ma tukunna hajiya,nan bakiga komai ba”
“Koh ?”
“Uhm”
Suna cikin zancene aka ƙariso daidai inda hanya zata hau sama,tasha ce a wajen cike da mutane,drebobi kala kala,wasu suna saƙƙowa da motoci,wasu kuma suna hawa dasu.
Faka motarsu sukayi a gefe inda iyani tacewa Iliya ya tsayah,ita kuma tafita zuwa wajen direbobin.
Bata daɗeba sai gata tadawo wajen gefen hajiya zeenah.
“Hajiya munyi sa’a,munsamu drivern dazai haura damu,mungama ciniki dashi kuɗin zaki kawo a bashi.
Lokacin da Iyani ta faɗi kuɗin saida Hajiya zeenah ta zare ido tareda cewa.
“Ke wai wane irin driver kenan,inada driver ki hayomin wani yanzu nan kuma ki zugamin kuɗi,?”
“Hajiya wanann ai yayi kuɗin aikina na shekara,hauka ake?”
Iliya ya faɗa cikin ƙufula,ganin kuɗin da ake shirin bawa wani kawai ya haura dasu,bayan shi duk abinda yayi a shekara kenan.
“Haurawar banza,muja motar mu mana mu haura da kanmu,dole sai wani ya haura damu,shekara da shekaru muna tuƙi duk a haka zai tsayah”
“Toh koh daga haihuwarka kake tuƙi,babu ta inda zaka iyah haura hawan mambila batareda ka faɗa,abin ya wuce yanda kuke tunani…..,..Hajiya ki bashi kuɗin ya haura damu,idan ba haka ba wasu zasu hayeshi,saidai mu jira zuwa nan yamma kuma in wani ya saƙƙo”
Hajiya zeenah tanajin haka ta ciro kuɗin ta miƙawa iyani,bawai kuɗin ne batada shiba,kawai yanda ta bada kudinne a abunda bai cancanta ba take jin takaici.
Saidai kuma ya zatayi,iyani tariiga ta ga logonta,indai akan cikar burinta ne,ko ya ninka wannan ma zata bayar,yanzu ma jin zasu jira hardai yamma ne yasata miƙa mata kuɗin.
Shikuwa iliyah ganin dagaske kuɗin za’a bawa wani lokaci guda,yasashi jin takaici a ransa,har yafara yankewar cewa zai dawo wajen da aiki.
Bayan iyani ta tafi da bashi kuɗin,sai gashi sun dawo taredashi,kansa irin cibi cibi ɗinnan,baki baƙiƙƙirin,gashi irin mutanennan ne kaman iska zata huresu,cikin ƙaƙau kamar itace.
“Heee hajiya gaskiya fah kinyi sa’a mace kika turo akayi cinikin,bilahillazi da banni da tausayi akan mata koh ninkin wanann kuɗin bazan karba ba,dandai ina son kaiwa balance wajen ogah ne a yau,shiyasa ma na karba wallahi.
Yaya kun shirya ne mu haura,ko kuma zaku sake shiryawa”
Ya ƙarisa maganar yana cize baki”
Zaro ido Hajiya zeenah tayi tana kallon iyani,wacce bataji tsoro ba kaman itada drivern. Wai wannan ne zamu shiga cikin mota ɗaya dashi muyi tafiya?
Ganin sunyi shuru basuce komai bane yasashi buɗe gaban motar yana shirin zama akan iliyah.
Sauri yayi ya matsa,yayinda wani warin gardawa ya bugeshi,cikin ƙanƙanin lokaci ya kaure cikin motar.
Koƙarin toshe hanci Hajiya zeenah takeyi,saidai kuma tana tsoron su haɗa ido da sabon mutumin ta madubi,yagane danshi suke toshe hancin. Tunda ya takalleshi sau ɗaya wani mungun tsoronsa ya zartu cikin zuciyarta,batajin zatayi gigin tunzura zuciyarsa bare taga mazayyi.
A wajen iliyah ma hakan take,abinne yabashi mamaki ganin yanda yakusa zama akan cjnyarsa,amma ko kulada shi ma bayyi ba,hankalinsa yana kan motar daya shiga yanzu.
Abubuwan ta ya fara duddubawa yana wage baki,da alama yanayin motar yayi masa yanda yakeso.
“Heeeehuuuu kai kai,rabona dana tuƙa lafiyayyar motar zuwa gembu harna manta,kullum saita yan iskan direbobin hanyar nan,amma yau kam za’ayi ɗiba tafiyah bilahillazi,irin wannan mota haka mai girma?”
Ya faɗa bayan yagama kurma ihun,sanann kuma ya ƙara da dariyah irinta tantirannan.
To to bil’adama a ɗaura belt maza,zamu hau ga sansanin aljanu,yanzu zamu fara da sama ta ɗaya,har zuwa sama ta takwas,daganan kuma sai ayi gangara,wanda bayason yayi karoda abinda zai dunga farautar mafarkinsa,wato masu ƙananan kuruwa a cikinku su rufe ido,zamu fara aiki.
Duk maganar dayake kallonsa kawai suke,da duk cikinsu iya iyanice kawai tasan mai yake nufi,ita kuwa batasamu damar faɗa musu abinda yake nufi ba taji yafara jan motar. Dan haka iya faɗamusu tayi su suka belt,daganan kuma aka fara tafiyah.
Giya ya danna tareda takar motar ya ɗorata sama.
Ganin yanda yake shirin takar motar kaman yasameta a jari bola,yasa iliya koƙarin yimasa magana,saidai tun kafin yace komai yaji kaman an ɗaga motar a sama,saboda yanda suke ƙoƙarin hawa wani uban tsauni dayake gabansu.
“Hahhhah inason kallon wannan yamayin a fuskar abokan kasuwan ci,karku damu domin ƙiran sunana ku zageni,kuna cewa karka kashemu tsinannan Allah,banshiya mutuwa ba wayyo……to kuce min TORO sunan kenan,kunga zaku fi daɗin cewa ”Allah ya tsine maka toro” ihu shagali”
Yana gama faɗin hakan kuwa ya hango idon Hajiya zeenah,wacce tamanne a jikin kujerar bayan,idon ta sun firfito kaman an jijjiga bera a buta……
“Hajiya tundaga hawan farko har kin yi laushi,todai karki manta ki adana kuɗinki fah,don kowanne hawa akwai nasa ƴan fashin,in bakida kuɗi a miki dukan kuɗin.
Yawan hawanki da shiga duhuwar dajin gangirwal,yawan gamuwarki da rabonki………muje zuwa……

 

🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
ƴar mutan jama’are

 

 

 

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Back to top button