Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 43

Sponsored Links

 

 

 

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣3️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

    Ya musa ne a gaban
Abba zaune matarshi tana gefe daya zaune bayan sun gaisa ya kalli Abban yana
fadin yau zamubi jirgin sha biyu zuwa sokoto na buga waya a turo mota azo a
daukemu.

    Kaidawa ke nan
naga jafar ya tafi tun jiya dani da zahra zan mayar da ita gidane ya fada kai
tsaye ba tare da jin komai ba.

   Abban ya kalli hjy
karima din yana fadin har ta gama hutun ke nan zata koma kafin tayi magana ya
Musa din yace eh zata koma don next monday zasu shiga school.

   Abba ya kara kallon hjy karima din sai cewa
tayi amma ai naga bashi ya daukota ba ya kamata ko in san cewa zata koma in
mata shirin da zan mata din a bangarena.

  No ku barshi ba sai
kun mata wani shiri ba ai ya mike yana fada fuska daure tare da fadin yau din
zan mayar da ita gida na fada mata ta shirya ko.

    Shiru sukayi ba
wanda yai magana a cikin su saida ya fice take fadin abinda yaron kan nan ke
mun bana son shi ina ruwanshi da zahra tunda ba wurin shi tazo ba.

    Amma ai kinsan
halin musa tunda yace zai mayar da ita gida yau ba fashi ke nan ki kyalesu ya
mayar da ita din tunda sun kitsa hakan  a
tsakanin su.

    Duk ina labe ina
jin abinda suke fadi a lokacin hakan yasa na koma nayi kamar ban san da zancen
tafiyan ba sai gata tashigo min dakin a fusace ta sameni nayi kwance ina
karatun wani littafina.

   Ta turo kofan a
fusace tana fadin Zahra wai me haka ke nufi ne nifa da alheri na daukoki ba don
sheri ba amma naga ana son a munafunce ni kuma ?

    Na dan kalleta
cikon mamaki ina fadin Mommy meya faru tace naji wai yau din nan zaki koma gida
yayan ki na fadawa Abban ku nace yau mommy ?

   Kamar ban san da
zancen ba ina dan dagowa ehmana yanzu yake fadawa Abban ku hakan nace gashi ban
ko shirya ba ban hada kayana ba ai.

   Au kema baki san da
zancen tafiyan bane ko me na girgiza kai tace shirmen banza toba inda zaki don
naga shi a gadarance yake abinsa ni ba irin iyayyen sa bane don ya sani.

   Nace a a mommy ki
bari in tafi tunda yace hakan ina jin tsoron ya musa sosao kada yai min fada
kawai na tashi na fara hada kayana dake watse a cikon dakin da sauri .

  Ta tsaya tana min
kallon mamaki kafinta juya ta fice a fusace kamar yadda ta shigo dakin da farko
a hasale na kara hada kayana wanan ne silar barina abuja a ranan sai ganin mu
kwatsam akayi mun dawo gusau baki a laikum.

    Ga ya musa yasa
Abba ya bada kudin da za a sai mun tsaraba Abban ya bashi shi kuma ya miko min
su duk da muka bar gidan ya biya dani wani tsore nayi sayayya sosai a store
din.

    Ummah tayi mamakin
ganina tunda na shigo ban zauna ba na nufi part din mama na gaida ita mun gaisa
sama sama tayi min an dawo lafiya na fito.

   Nan ta fara sake
magana cewa ai ido ta saka muna dagani har ummah ita zamuyiwa munafucin mu nuna
muna tare da amarya don a hade mata kai aga bayanta a gari ko ?

    Kai haba mama
yarinyar da Abba ya tilastawa da zuwa Abuja dole wai a can yanzu zata rika hutu
don kawai an mata sherin cewa wani saurayi na zuwa wurin ta suma fa bada son
ransu bane tatafi abujan hutu.

    Aiba sheri bane
don nina fadawa Alh komai na sanar dashi kada yaji yace an munafuceshi daga
baya don tana ganin yaron da zubin fulani take wani dagawa mutane kai don
rainin wayau.

   Haba mama hakan ai
bai dace ba tunda abinda takeso shi za a bata ta aura ai don baida kudi ai ita
ta ganshi tace tana sonsa sai a barta da abinta ta aura.

   Nima saidana fada
maki mama ki kyalesu suyi abinsu ba ruwanki ba ita zata sha wuyanta ba ita
kadai ina ruwan wani ya musa din ya dan harari Aishan yace .

    Shi auren ne wuya
ko auren wanda baida zarahi haramun ne akace ai shike nan taje ta aureshi din
meya damu maimuna mama din ta fada sai ya jafar yace shine ai mama ki kyalesu
please tunda tace shi take so.

   Bayan fitan diya
mazan daga gidan suka zauna nan da Aisha suna magana suna dariya tace ai barsu
na fisu iskanci zasu raina kansu daga ita har uwar nata.

   Ba mayana zai shigo
wani sati ba ku fadawa masu neman ku cewa suzo suga Alh din nasan idan ya
matsesu babu wani shi zasu fitar hakana din ai kinga ta fita zakka a cikin ku
ke nan.

   Shina so ki gane
tuntuni mama baki gane hakan ba ai wanan zaifi masu zafi da ciwo ace kowan mu
ya auri abin kwarai ita ko ta buge ga wanan tallakan karshe.

  Kai Allah ya rabamu
da kishiyar uwa mara imani macen da bata kaunan ganin diyan kishiyanta su karu
da alheri ko wani iri amin.

   Nikan tunda na
shiga  dakina na fara gyara duk da baida
wani datti a cikinsa na gama komai nayi wanka na dawo na kwanta ina tunanem
irin makircin mommy da abubuwan da suka faru a tsakanin mu a tafiyana.

    Tare dashi akai
sallah asuba don haka wasu suka sanda dawowan shi garin sai binshi mutane keyi
da kallon mamaki har ya koma gida duk yana kule da hakan da mutane keyi mashi.

   Kwanciya yayi don
yana tare da gajiya sosai lokacin barci ya dan fara diban shine yaji muryan
malam Tanimu da labarin dawowanshi ya sama ya garzayo ya ji labarin komai daga
bakin shi kafin wani ya bashi labarin yadda akayi.

   Sama sama ya dinga
jiyo sallamanshi kafin yaji muryan Dije ta fito suna gaisawa dashi yaji yana
fadin ace Amadi ya dawo shina niishigo taro nai.

    Badai lahiya ya
iso ba ya yunkura a lokacin zai tashi yaji amsan da Dijen ta bashi yasa ya koma
ya kwanta yana sauraren su dije din na fadin .

   Allah ya dawo dashi
lahiya kasan dan yanzu da wayau shi yana wurin neman shi ana nan ana masa sheri
da kazzalaha a cikin gari har wanda baka zata da zai maka sheri ba sai kaji
mugun zance da mugun nufi a bakin shi.

   Hakane kan Dije
kesan in abu yazo sai mutum ya dinga tunane har ya fita cikin lissafinai adaiyi
hakkuri abinda ya wuce a barshi ya wuce a yafewa juna tunda ana tare wuri daya.

    Shikan amma abin
ne da mamaki wai wanda ka dauka jigo shikama zagon kasa a boye yana hwadin
maganan da bai dace ba a kanka dolena rai ya baci.

  Yanzu dai kiyi
hakkuri ina shi Amadin yake shina zaka in gaisai in ya tashi ina hwada mashi ka
shigo naji ya koma ya kwanta dazun don hakane malam tanimu din bai samu ganin
Amadin ba wanda baiso hakan ba a lokacin.

   Sai bayan tafiyan
shi an dan dade ya fito ya samu dije zaune bakin murhunta tana hasa wuta suka
gaisa yake fadin yaji muryan malam tanimune ai.

  Bar munafukin banza
da wofi watau yaji labarin dawowankana shina ya taho ya samu na karaswa aini
malam Tanimu ya bani kunya a garin nan .

   Wai ace shi da
kansa ke yawon bata muna suna yana aibanta maka sana ,anka da wani manufanai
watau dama ashe dariyan hakori da jinine a tsakanin mu dashiya.

   Saida haka ya
kasance na gane masoyan mu na gaskiya da wa yanda basu son mu da alheri a garin
nan kai Amadi naga abu a cikin garin nan bayan tafiyan ka nan ta dan bashi
labarin irin abubuwn da suka faru shidai
murmushi yayi kawai bai samu abin fadi ba lokacin.

   Can ya mike ya
shiga dakin dije din ya kwaso kayan daya shiga dashi jiya cikin dare nan ya
dinga fitarwa yana mata bayanin komai a tsanake.

     Ya kwashe ya
mayar daki Dije sai faman saka mai albarka da takeyi tana mashi adduan gamawa
da duniya lafiya yana amsawa son shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyarshi
lokacin kan komai.

   Dakinshi ya nufa
duk da ba wani kayan kirki a ciki hakaya gyara ya kakabe dan kuran dake ciki
saida ya fitar da komai ya kakabe ya mayar ya koma gyaran gida ya gyara ko ina
don duk gidan ya yamutse kamar ba wani mahalukin dake rayuwa a cikin gidan.

   Hakama dabbonin duk
sun rame da alaman basu samun kiwon daya dace a bayanshi nan ma ya gyaro ya
zuba masu dan abincin daya gani a wurin.

   Yana kule da kallon
da uwar garke ke mashi tun safe amma addua ni a zuciyan shi sam bai nuna ya
gane hakan ba gareta saima nunawan da yayi bai damu da itaba..  

    Baiyi aune ba yaji
takai mai irin tunkudan data taba mai a baya a mambilla hakan yasashi juyowa
gareta yana dan tsura mata ido na dan lokaci kafin ya mika mata sauran abincin
daya rage a hannun shi din.

   Daga haka ya juya
ya bar wurun bai sake juyowa inda dabbobin suke ba ruwa ya diba ya watsa a jikin
shi ya fito ya shige dakin shi ya shirya lokacin ya nufi dakin Dije don ya
karya.

    Bayan ya zauna ya
fara cin abincin ne ya dago yace mata kinji labarin Rashida dacewa
mahaifiyarshi don haka yake kiranta da sunanta.

   Mamaki Dije taji
jin ya tambayeta mahaifiyar nasa da bai damu da yin hakan ba garesu tace dashi
ta bugo waya tana tafe don an kirata an sheda mata batan ka .

   Wai mijin natane
maciji ya taba ashe muka jisu kwana biyun nan shiru amma tace da sauki yanzu
zata zo nan bada dadewa ba idan ta samu sararin hakan.

   Allah ya kyauta
yace da ita yaci gaba da cin abincin shi yana nazari kafin ya sake dago kai
yana fadin lokacin da ta rabu da mahaifina ina da shekara nawa ne Dije ?

    Kai Dije ta dago
tana mashi kallon mamaki kafin tace dashi missa ka faye tambaya akan mahaifinka
yanzu mutumin da yai tafiyan shi ba kara waigo inda kake ba .

  Ko bai taho nan don
kowa ba ai zai taho don kai amma tsawon shekarun nan ya kwashe ba tare da yasan
ya bar wani halittaba a nan

   Koma meye shidin
dai mahaifinane ko Dije banda wanda zanyi tunkaho dashi a duniyan nan bayan shi
banda wanda zai tsaya min ya zama min gatana a al,umma bayadashi.

   To wai miya kawo
wanan maganan yanzu kuma ina kule da cewa tunda ka fara girma ka dauki ranka ka
dora akan shi ka daina tuna wanan mutumin.

    Dole in tunashi
Dije tunda an fara shegantani cikin garin nan ana kirana da mara asali mara
gata a idon mutane duk da nasan ina da gata gatan da ba kowane keda shiba garin
nan.

 A kul akul naji ka
kara fadin wanan haukan waya isa ya sheganta min kai duk garin nan in maka na
mahaukaci bayan kowa yasan da auren sunna ma,aikin Allah aka haifeka.

    In hakan yasa ka
fara haukan hasashen maihaifin ka nada gata ko wani abu gara ka daina tun wuri
don wanan kan ba gaskiya bane haka yazo garin nan fakirin shi.

   Wanda na tabbatar
da sanadin haihuwankane ma ya kawoshi garin nan ya biyo yan zuwa kudu yazo nan
ya zauna tare dasu a karkashin  Alh Akilu
mai shanu.

  Har Allah ya
taimaka  don darajan Alh da uwarka ta
nace saishi aka dauketa aka bayar da ita amma kamar mai bakin uwa ana zaune
kalau haka kawai da rana tsaka ya bijiro da barin garin nan kamar mai aljannu a
kanshi ko kurciya ba yadda malam baiyi ba amma ya kyankyashe yace shi tafiya
zaiyi.

   Allah ya kyauta ya
fada ya mike ya fice daga gidab lokaci guda kai tsaye waje ya nufa duk wanda ya
ganshi sai ya tsaya yana kallonshi don labarin shi daya karade garin na batashi
da kowa ya sani.

   Ya dai sha tambaya
da kallo kafin ya isa kasuwa ya sayowa dabbobin su haki ya hauwo mashin ya dawo
gida zakace yadda yai wani haske ya murje yayi kyau kamar inda ya fito a cikin
AC yake kwana yake wuni yadda yai kyau din.

   Haka yasa mutane ke
kara mashi kallon mamaki inda duk yabi bayan ya kawo masu abincin ya sake fita
zuwa wurin oganshi na kasuwa suka dan tatauna dashi din a can.

   Wallahi na gaji
Yabi wanan tafiyan ma da kyar nakeyin shi a yanzu duk katarana ya zoje wurin
hawan tsaunin nan dafata tayi ba tare data iya bata amsa ba  ga magananta ta dan taka wani dutse ta haya
tana mayar da numfashi da sauri sauri ta fara fadi.

    Adda Wuro da badon
bukatana bane ba yadda za ayi ace na hawo wanan wurin amma ba yadda na iya
tunda ina son bukatana ya biya .

    A rayuwana na
tsani in bude ido inga anyiwa diyana yan uba a duniyan nan dubama ga yanzu
yadda dukiyan Alh ke kara bunkasa sosai yanzu.

   Ba zan zauna ina
gani ba wata ko wani yazo daga sama yace zai cudanya damu da sunan inuwa daya a
karkashin Alh ko ita wanan jakar na bartane ta zauna kamar yadda mai allon
karfe ya umurceni dayi a kanta.

    Na riga naba kare
mahaifanta ya cinye don haka yanzu banda fargaban komai a gareta tunda
mahaifanta karnuka sun lashe shi tuni bata da sauran amfani a yanzu. 

   Kai Yabi baki da
kyau kiga yadda matan nan tayi kamar zata mutu lokacin nan kuwa amma kika nuna
kina tausaya mata kene har da fita kasan waje da ita.

    Saida hakan ne
Addah wuro mazan yanzu in kayi sake kaine a baya balle irin nawa mijin da idon
shi akan mace har indai yaga mace yana so yanzu zakiji zancen aurene.

   Amma yanzu kinji
shiru ba wanan zancen tundana hada shi da makulli na kulle na kada wanan tsohon
rijiyan baki kara jin wani zancen aure ba kuma gareshi.

  Haka suka sukai ta
hira tsakanin su har suka isa bakin bukkokin dake tsakiyan amtsaunin da alaman
mutanen wajen su dan wayesu nan aka gaisa akai ya kwana biyu.

  Basu sha wuya ba
wurin ganin bokan don yasan zuwansu wurin shi alherine garesu shida iyalan shi
gasu dai fulanine amma kuma arnane su basu ko wani irin addini a rayuwan su sai
tsafi.

  Zaka kuma samesu da
dan walki a jikin su mazansu da matansu ga tarin dukiya da Allah ya basu a
tsakiyan dajin sun gabatar mai da abinda ya kawosu duk da yaga abune mai wuya a
iya dakatan da hakan .

  Amma sai ya nuna
masu zaiyi aiki mai wuya ya hana hakan faruwa ya dai dan kwantan masu da hankali
tare dayin surukulen jayewa Alh hankali ga barin wanan maganan .

   Sukai mai sallama
mai tsoka suka dawo a gajiye ace tsafi gaskiyan mai shi saiga Alh na fadi washe
gari ta shirya su koma Abuja ya gaji da garin nan shi.

  Haka suka tattara
suka koma ba wanan zancen nan ya bar Jabbi da dan baro da mamakin yadda akayi
lokaci guda Alh yabar zancen yaron daya tasasu a gaba a cikin yan kwanaki biyun
nan.

   Duk da haka  basu share zancen ba a bangaren su don sunci
gaba da bincike a tasu bangaren saboda sanin halin hjy Yabi da sukayi don irin
hakan yasha faruwa a tsakanin suma ganin haka suka kulla da ita.

  Har suke kwato
abokin nasu daga halakanta idan tayi wani abin sai subi su warwale ba tare da
sanin aminin  nasu ba.

   Wanan yasa ta
tsanesu da duk wani abu daya shafesu duk inda ta buga kuma sunki rabuwa suna
manne dashi ko yaushe don har abuja sukan bishi wani lokaci duk da sun san
tsanar da take masu din.

   Don hakane ma wanan
karon basu tsaya bin ta kanshi ba koda ya tafin suka samu isah tella yai masu
bayanin unguwar da yaran suke suka bashi sallaman da sukai mai alkawari suka
tafi.

   Ni dai an wayi gari
naga sauyin fuska tsakani na da mama sai hakan yasani shan jinin jikina amma
ban yarda na fadawa ummah komai ba.

  Haka abinda ya faru
dani da mommy ban mata hiran komai da naji ba kona gani saina barwa cikina
zancen har muka koma school mukaci gaba da karatun mu kamar yadda muka saba.

   Saidai karatun
yanzu baija sosai don rashin Ahmed da bai samun shigowa yana muna bita ko
yaushe a yanzu busy yake wurin neman kudin shi.

  Mun dai hadu dashi
sau biyu ya dan taba muna karatu daga nan bamu sake ganin shi ba kuma da mukai
waya dashine yake fada min cewa ba zama garin ne yana yawan shiga kauyoka har
wasu jahohin suna sayo hatsi.

Leave a Reply

Back to top button