Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 39

Sponsored Links

CHAPTER 39

Kuka take sosai dayayi sanadin samun gefen titi ya parka motar,ya juyo ya fuskanceta da kyau ya sauke gauron numfashi yakira sunan ta da Aisha.

Bata amsa masa ba sai kallon sa datayi da idanun ta masu tsiyar da hawaye”kiyi shiru ki share hawayenki idan har wannan aikin da nakeso muhaɗa karfe da karfe dan ganin mun taimakawa al’umma waƴanda ake zalumta da ƙananun yara basuji ba basu gani ba ne be miki ba sorry ki dena kukan haka is ok zanyi komai da kaina dan ganin na gurfanar da waƴan nan azzuluman gaban ƙuliya.

Aisha sun maida ƙananun yara da dama marayu sun maida mata dubun dubata zawarawa haka zalika sun kashe marasa lefi sunyi garkuwa da wasu sunwa wasu kisan gilla.

Aisha ko kinsan mahaifinki yana raye be mutu ba tsayon wannan shekarun.

“What
Shine abunda yafita daga bakin ta hawayen idonta yatsaya cak ta waro idanunta kaman zasu faɗo kasa.

Alhaji shehu
Cikumo fadila yayi da iya karfinsa ya shaƙe mata wuya yace”oya faɗamun me kikawa Aisha da zakice mun ta ɓace tsawon wannan lokacin basan idan suka shiga ba.

Fadila ido ya raina fata taji shaƙa iya shaƙa sai kakari take sannan ya saketa ta faɗi kasa jikake tadafe wuyanta sai tari take.

Faɗamun abunda kikayi mata yafaɗa cikin daka mata wani gigitacce tsawa dayasa hanjin cikinta hautsunawa ba shiri ta shiga cewa”ni ni ban mata komai ba asalima tunda suka zo mun gaisuwar mutuwar innata bansake jin ɗuriyarsu ba,kumama ai ni bance zan mata wani abun ba.

“Karya kike baƙar munafuka ya katseta da faɗi haka cikin nuna jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye daga duƙen da kake tace”naji ni munafuka ce kai kuma fa?
Karfa ka manta kaine nan wanda ya canzan ra’ayina kan ƙawar da bani da kamarta.

Saida ka gama da ni da rayuwata yanzu kazo kace Aisha kake nema zaka aura kaima kasan muddin ina numfashi a doro duniyar nan to wallahi wallahi ko Auren wucin gadi baka isa ka auri Aisha ba.

jikake ta tass sauka mari daya hanata karashe maganan bakin ta,isowar yayanta Sani wajen yasa Alhaji shehu barin wajen ba tare da ya bashi amsan tambayansu da yake ba.

****
Kace mahaifina yana raye?

“Kwarai ya amsa mata

“Taya zan yarda da maganarka?

Shin idan da gaske mahaifina yana raye ina yake yanzu?

Kaga dan Allah yaya faisal idan kanason amfani dani dan cimma wani manufarka ta aiki karkamun karyar mahaifina yana raye ka yaudaren ta wannan.

Tana kaiwa nan ta rufe fuskarta da tafukan hannun ta ta shiga raira kuka ina mai tsuma zuciyar mai sauraro ba komai take yiwa kuka ba sai famin miƙi da yanzu akai mata na rashin mahaifinta sai kuma tunawa da tayi da Anna uwa ɗaya tamkar a dubu yanzu ko ina take?

Shin tana cikin ƙoshin lafiya ko ya?

Kode itama waƴan nan azzaluman sunyi nasaran kamata sunyi garkuwan da itane.

“La la la la la ina hakan sam ba maiyuwa bane ta furta da karfi sai kuma tashiga marin kanta da kanta tana kuka takoma masa tamkar wata mahaukaciya sabon kamu duk tagama birkice masa,tayi daya sanin sanar da ita yayi duk da dama abokin aikin sa samuel tun farko ya gargaɗe sa da karya kuskura ya sanar da ita harsai sun samu gamshesshiyar bayani akan yana rayen ko sun ganshi sannan ne.

Amma gashi yanzu yazo ya ɓata goma be gyara ko daya ba.

“Aisha ki nutsu karki bari hankalin ki ya gushe akan abunda ni nasan gaskiya nake faɗa miki kuma na miki alkawalin haɗaki da mahaifinki muddin na binciko nasamo inda yake koda ba zakiyi aikin nan da mu ba.

“Kaga yah faisal karabu dani da banzan ƙudurin ku na aiki,ni nasan da ace mahaifina yana raye da bazamu ɗauki tsawon shekarun nan bamuji ɗuriyar sa ba.

Anna tasha faɗamun duk ranan da Abba ze bayyana kansa to tabbas zeyi wani abu da ze girgiza waƴan nan azzaluman koda ta hanyan fallasa wani sashi na sirrin su ne.

Anna tasha faɗamun haka wannan dalilin yasa koda yaushe nake cikin kasa kunne na saurari labarai duk da bani da waya amma koda yaushe ina tambayan mutane wani sabon topic ne wannan yake bada wuta a media amma shiru kakeji.

Sai yanzu kawai dan ka karanta wani shashi na ƙundin sirrimu kace xakayi amfani da wannan daman wajen son juyamun da hankali

Yanda ta birkice masa dole tasa ya kyaleta dan yasan tana bukatar hutu ba ita dake da ƙarancin shekaru ba komai yawan shekarune ba lalle ne ya yarda da shi lokaci guda ba.

Alhaji sunusi
Suna zaman meetin da wasu manyan abokan harkallan sa,daya daga cikin mai suna Alhaji hamza ya kalle su yace”gaskiya Alhaji ba yanda za’ayi musaka maƙudan kuɗaɗen mu munaji muna gani muxo muyi asarar su ba.

“Haba Alhaji hamza wani irin asara kuma?
Bayan ba tun yau muke wannan sana’a da kuba,ko ba haka ba Alhaji ɗahiru?

Numfasawa Alhaji ɗahiru yayi yace”gaskiya Alhaji sunusi maganan Alh hamza yana kan hanya karfa muzuba kuɗaɗen mu daga baya muzo mutashi a tutan babu wato ba tsuntsu ba tarko.

Kayi sake Alhaji ishaq ya kubce daga hannun ka ka kuma san wannan babban barazanace garemu baki ɗaya,kaxo kace kaga matar sa harda ɗiyarta itama kayi sake sun gudu ba gansu ba.

Kafasan ance jada baya ga abokin faɗa ba tsoro bane wata ƙila shiryawa zasuyi kuma kasan duk sirrin ka yana tafin hannun Alh ishaq kai ba kai bama hatta mu damuke tare dakai dakyarne zamu tsira idan ƙwan tafashe.

Sharce guminsa yayi yace”ina da plan sosai akan wannan ba abunda ze samu kuɗin ku sannan wannan aure da nakeso na haɗa tsakanin ɗiyata da ɗan Alh badamasi shima yana daga ciki dan cibiyar alhakk zata dawo karkashin kulawarmu sai yanda mukai da shi karshe shikuma mu turashi inda bazuwa idan yace ze kawo mana matsala hhhhhhh dukansu suka kwashe da wani irin dariya wasu bosawa.

Leave a Reply

Back to top button