Hausa NovelsTUMFAFIYA Complete Hausa Novel

TUMFAFIYA 47

Sponsored Links

 

 

L

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[3/7, 10:12 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,

🌱TUMFAFIYA SIRIN KI     SAI ALLAH
,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4️⃣7️⃣

ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,

 

  Basa jin hausa sosai
sai filatanci don haka ba wai lalai bane wani ya zauna dasu yayi hira ga maganganun
da yan uwan mahaifiyashi ke son yi dasu Amma rashin jin hausan da suka nuna
basaji yasa sun barsu dama kuma gaisawa kawai akayi ya gabatar dasu gun yan
uwa.

   Daga nan ya kaisu
masauki inda zasu sauka sun kwana washe gari karfe goma suna falon Abba zaune
suna ganawa dashi inda Abban yasha mamaki ganin yaron ashe da gatanshi .

   Ba bata lokaci suka
gabatar mai da sadakin aure sukace kaya mata zasu kawo idan a ka gama hadawa
sukai sallama suka barsu Abba da mamakin hakan a gaban su ya musa akai komai.

    Dan uwan Abbane ya
kalleshi yace dama na fadama in kana bin zancen mutane kai zaka kwana a cikinsa
yaron nan kowa yasan ba shege bane da ubansa.

    Ya kamata mutum
yai amfani da iliminshi na zamanin nan kada a kaishi a baro shi yanzu gashi
kaso kuresu ko ka tozarta uwar yan nan da ita yarinyar har yaron kaga Allah ya
karesu.

    Shiru Abban yayi
shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyarshi game da hakan don shi har yanzu
laifina dani da ummah yake gani.

   Basu fadawa kowa
zancen zuwansu ba saida dare ina kwancene ummah ta shigo dakina tana fadin kizo
Alh yana magana damu a falonshi.

   Gabana nd yayi wani
irin mugun faduwa ta juya ta fita ni kuma na mike na saka hijabi a jikina na
fito ummah na gaba ina binta zuwa part din Abba din dake neman mu gabana sai
faduwa yakeyi  a lokacin.

   Ashe kusan kowa na
gidan namu kaf suna falon Abba sin nida ummah ce muka shigo a karshe don haka
kusan kujerun duk an zazauna kowa na kallon mu yasa ya musa da ya jafar mikewa
da sauri.

   Suka kwashe
tarkacen kujeran dake kusa da Abba sukaiwa ummah wurin zama dama sauran matan
nasa duk sun hakince saman kujerun kusa dashi sai gashi yanzu ta fisuma zama
kusa dashi din sosai.

    Don ita a kujera
daya suke da Abba din mama cika take daga inda take zaune  tana hararan yaran nata dake faman rawan jiki
kan ummah din ta samu wuri yadda kowa ya samu.

    Nikan na zauna
kusa da inda kafan ya musa yake na dukar da kaina kasa don jikina ya bani cewa
wanan zaman akaina akayishi don yadda naga kowa na gidan ya hallara sai yan
kanne uku da suke kananane ba a kira ba.

   Mata mu godewa
Allah idan kin samu haihuwa da wuri mussanman uwargida koba komai yayan nan
zasu zame maki katangan dafawa a wani wajen.

  Don nasan da ace
ummah Allah yaba haihuwan wuri ta haifi yara da yanzu kidon dole Abba ya daga
mata kafa a wani wajen.

  Don yadda naga mama
tana shakan iska sosai yanzu tana nuna tafi kowa komai a gidan sai abinda tace
dole kowa zaibi.

   Wanan kuwa ya samo
asaline da yayan ta maza manya da yanzu take ganin su wuce sanin kowa a wurin
Abba din.

   Can Abba din ya
dago yace OK kowa yazo ko eh dama su ake jira ai gasu kuma sunzo OK dama na
tara ku nan ne badon komai ba sai zancen auren yaran nan daya taso musanman
naki ke zahra ya kira sunana karo na farko har yasa na daga kao na dan kalleshi.

   Yaci gaba da fadin
kada ki kuka da kowa duk abinda kikaje gidan yaron nan kika gani ki kuka da
kanki don kece kika zabo abinki kuma na baki shi.

    Ummah ta dago kai
ta kalleshi ashe Abban ya ganta yace yes da in zauna ta jawo min wani zance
gara kawai na mika mashi ita suje can su karata a gidanshi tunda ita tafi
karfina yanzu.

   Kuka na sake lokaci
guda yace ai baki kuka ba sai kinji dokokin da zan kidanya a kanki yanzu don ba
zan sayar da akuyana ba ta dawo tana ci min dangan gidana daga baya kuma.

   Don haka abinda
nake nufi a nan shine ban yarda wani ko wata yace zai taimaka maki ba daga
cikin dukiyana  har idan naji hakan zan
sabawa mashi fiye da tsamaninsa ko waye.

  Abba ya musa ya fada
sai ya dagawa ya musa din hannu mama tace kai wani irin tsagerana wai ubanka na
magana komu matanshi ba wanda yai magana sai kai.

    Amma mama kinji
abinda Abba yake fadi sai naga wanan dokan kamar yayi tsauri da yawa ga
yarinyar nan kowaye ma aisai ya nemi taimako a wurin wani balle ita da zata
auri wanda baida karfi.

    Kai kaimin shiru
ko yanzu ranka ya baci a nan na fada na kara kada wanda ya daukar min wani
abinda ya fito daga tsatsona da sunan taimakawa zahra dashi.

  Ai tunda ka fada an
gama dama ai don ka akeyi inji mama don me za a taka dokan ka kuma,  sai hjy karima tace amma dai daka sasauta
dokan nan a kanta don Allah   .

    Iya zancena ke na
sai zancen kaya don kada uwarki tace nayi bambanci su wa yan nan na riga dana
masu sayayyansu a Dubai tun lokacin da suka tsayar da mazajensu don haka a yanzu
banda lokacin komawa Dubai nace zan sayo maki kaya acan anan Nigerua nasa hjy
karima ta duba maki kuma kayan zasu shigo wani sati sai ya fada maki inda za a
aje kayan.

    Idan yaga dama yai
maki lefe in kuma baiyi bama wanan matsalan kuce don ni na riga na gama
maganata a kanki ko kowa nan kuma yaji abinda na fada dai.

   Ya jafar ne da
hankalinshi ke kan waya zuciyasa na tafasa don rashin gaskiyan da yaga ana
shukawa a wurin wayan nasa yayi kara ya dauka tare da mikewa don barin falon a
daidai lokacin da ummah tace shike nan ko ?

   Tana tambayan Abba
din yace eh shike nan ko akwai wani magana ne tace a,a babu komai wallahi mun
gode Allah kara arziki yasawa auren su albarka ga baki daya sai ta mike don
barin falon.

    Ya musa ma ya mike
shima mama ko sai mere baki da takeyi tana kumshe dariyan ta hjy karima kuma
cewa tayi Allah kyauta abindai baiyi dadi ba wallahi.

    Dadin ke nan tunda
haka suke so ai an masu Abba ya fada a hasale ko waye yace ba zaiji maganata ba
haka zan masa kafin ya tozartani garin nan.

   

  Sheshekan  kuka kawai nakeyi na mike nima na nufi dakina
ban samu ummah a falo ba na shige ciki a yau ne karo na farko da zance nayi
bakin cikin fitowa daga cikin zurian Abba.

   Ba dan komai ba sai
dan irin tozarcin da yai min nida uwana a gaban kowa na gidan yana ji wanda
nasan hakan ba karamin nakasu zaija min a wurin dangina ba.

    Kuka kan dagani
har ummah munyi shi mun gaji sai hakkuri ni dai ba zance naga ummah na wani
shiri ba akan auren nan na fada na kara fadin hakan.

   Ashe abinda ban
sani ba shine zama da manya mata umma ta gano shirin da ake son mata don ta
gama fahintar kowa zuwa lokacin.

   Ta kuma gama shirin
da zasuyi ko a gidan tare da yan uwanta da aminan ta kallon kowa takeyi kawai
ta zuba masu idanu an kai kayan an jera washegari kuma kawar ummah tazo da nata
kayan aka kwashe wanan aka jera min wasu tare da kara gyara gidan suka saka ayi
abubuwan daya dace ayi.

   Abu mafi girma da
ummah tayi min daya dauki hankalim mutane shine saya min manya manyan freezer
guda biyu wanda daga shigowa gidan part dina sune zasu tare ka sai wani tsaye
na amfanina.

    Mai ilimin zai
fahinta iya fahintar shi da hikimar ummh na tanadar min abubuwa irin haka a
matsayina na matar tallaka da zan aura.

   Mama sai famkama da
isa da izza sukeyi zata aurar da diya cikin gata da sa,a gari kuma ya dauki
zancen bukin kowa da irin abinda yake fada a kan auren.

   Ya musa duk abin
rabo na buki da yai muna a ko ina zai daza hotunanmu mu uku tare da mazajen mu
zakaji ana fadan wallahi mun dace munyi kyau sosai a photon.

   Bansan inda hanne
ta samu labari ba sai ganinta nayi kawai ta fado gida  namu da ummah ta fara magana kafinta nufo
dakinda nake.

  Ummah abinda nake ji
gaskiyane wai zahra zatayi aure bata fada maki bane ko me ummah ta tambaya
sukai na dan arewa ka tambayeshi ya tamnayeka shima.

   Nan dai ta mike ta
shigo dakin ta sameni ina kwance naji sallamam ta don bansan ta shigo gidan ba
na dago ina amsawa do  na sheda muryanta.

   Amma zahra baki da
kirki yanzu ashe zancen auren ki akeyi har lokaci ya gabato haka amma baki fada
min ba ke nan ke baki daukeni a yadda na daukiki ba ke zuciyar ki ?

   Na dan harareta ina
fadin yanzun ba gashi kin ji ba har kin zo nima yadda kikaji hakan naji zancen
a bazata na kwashe yadda akayi na labarta mata ina kuka.

  Itama kukan takeyi
kafjn tayi shiru tana fadin zahra na fahinci sheri akeson kulla maku ke da
ummah.

   So ake aga iya kan
ku a nuna maku kuba komai bane a gidan sun manta hassada ko sheri wani lokaci
yana zama alheri ga bawa.

   Insha Allahu auren
ki da master alherine a rayuwan ki  yanzu
abinda nake so dake shine ki saki jiki don Allah mu fara shirin komai banji
dadin rashin fada min abinda ke faru haka da bakiyi ba. 

   Yanzu mai kuka
tsara keda master din game da bukin bamu tsara komai ba amma ban sani ba koshi
ya tsara din a bangarenshi.

  Gaskiya ban tsamani
yan uwanki zasu hada bukin su dake don haka mu zamuyi wallima a namu bangaren
walima wanda ya amsa sunan wallima duk mai zagin mu saidai ya zagemu zamuyi na
farko a gidan yan uwanki sai na biyun idan an kaiki zamuyi a gidan ki ko ya
kika gani ?

   Duk abinda kikayi
yayi daidai na bata amsa tace zan kira su manir musan abinyi yanzu kafin nan
barin je falo in shawarci ummah naji.

  Ta mike zuwa falon
wurun ummah na koma na kwanta ina lumshe idanuna lokaci guda tare da tuno
Abubuwa da dama a rayuwana.

   Amadi  bansan me zance da kai ba yanzu yaron nan
saida katai wurin yan uwan ubaka kagano su ?

   Duk da haka  na da kyau don zuaan yai muna amfani don sjn
taho su  fishe mu kunya a idon jama,a
masu maka kallon mara gata da baka da kowa yanzu saisu shiga taitaiyin su.

   To Dije mi zance
maki ai yanzu ke sani ko nan ya fara bata labarin yadda yayi tafiyan nasa bai
fada mata komai ba son ya boye mata abubuwa da dama a cikin hiran nasa.

   Ta nisa tana dafin
ashe habu mutumin asalina haka da gatanai ya baro gida zuwa nan rabon
haihuwanka na ya jawoshi.

   Don rabo in ya
rantse sai mai shi gaskiya shi nice wai ahin meya asalin waga diya da mutumin
nan ya baka na  ?

   Shin yarinyar nada
wani nakasu na ko tana da tabone yasa uban ya dauka ya baka don kowa dai yasan
bakakai matsayin auren diyanai ba.

   Haba dije yanzun fa
kika gama fadin rabo in ya rantse sai maishi wallae zahra yar arziki ta kema
kin sheda haka  ni kawai na dauki wanga
abu dai mukaddarina daga Allah.

   Duk cikin gidansu
ta fisu kyau da halin kwarai kawai sai rabona yasa mahaifin hushin zuciya don
kawai tana mu,amulan karatu da niya.

   Yan gulma suka
dauki zancen suka kai mashi wai soyayya ya tai takai da dan tallaka da farko ya
nemi da in rabu mai da diyatai nakumayi hakan.

   Amma kuma anka koma
anka hwada cewa ya tai har yanzu tana tare dani wai zan lalata ma wanan yasa
yai hushin zuciya yace ya bani.

  Ikon Allah a,a uba
ka hushi haka da diyanai irin haka ya dau yarshi yabawa dan tallaka kamar ka
Amadi nina dan tallaka amma dai kesan yanzu ina iya rike mata ko ?

   Ko huduna amma
banda diyan mai karfi irin wanan ina ya wanga gida taka iya zama gidan ga kasan
fa su a cikin dadi suka taso a rayuwan su.

   Dije amma aure ai
zata zo yi nan ko don haka tasan ba zama irin na gidan su na komai a baje shi
ba yadda rai kaso.

    Namijin duniya
alama dai ya nuna baka jin komai ga dauko yarga zuwa gidan ga ta zauna amma ni
ina jiya maka abinda zai tai ya dawo nan gaba.

   Don waga aure kamar
tonon asirina a garemu in baka iya riketa ba kasan sakinta zakayi abu ya dawo
ana dana sani a kanta.

   A,uzu billahi Dije
wane irin fatana kikayi muna haka jam banji bakinki ba walla ke da yakamata
kiyi muna addua ke hwadin wagga maganan yanzu ina ga mutanen waje can su mi
zasu hwada min.

   Ai suna nan suna
fadi batutuwa akan auren ga wasu cewa sukai auren jarina kayi wasu kuma hwadi
sukai kwadena ya kai ka da sauran su.

   Murmushi yayi ya
mike lokaci guda ya saka takalman shi dijen na fadin ina kuma zaka muna magana
kallon Dije din yayi yana fadin.

    Maganan ki bata
min rai yakai gara in tai zuwa inda yafi min zama sauraren wagga zance mi
ruwana da mutane wa kullMin lokacin da nike cikin damuwa.

    Allah ar samuna
wagga yarinya a sanadin komai gareni don itata ta hwara taimakamin a rayuwana
ta hito dani fili anka hwara sani na yanzu.

  Ni banda abinda zan
sakawa yarinya ga dashi sai fatan Allah ya bani ikon in riketa ammana inyi
fatan Allah ya ban abinda zan cisheta in tufatar da ita.

   Muma shina fatan mu
gareku dama abinda uwarka taka damuwa kaine na yasa na hwada maka don a san
abinda ake ciki kafin akai ga daurin auren.

    Babu komai sai
alheri in sha Allahu zahra alheri na a rayuwan mu baki daya dije ni dai ki
hwadawa mama ta tayini sonta yadda nika sonta.

   Yarinyar data
zabeni cikin dubu tace ni taka so mi a ban iya mata a rayuwata kamamin bakin ka
da bare bare tun baka san mi take ciki ba ka hwara sake zance haka.

   Juyawa yayi yana
kallon mahaifiyar shi dake tsaye kofan dakin tun fara maganan nasu da Dije din
sai ya soke kai kasa don baiyi tunanen cewa tana wajen ba lokacin.

    Ya juya a hankali
ya barsu suna maganan yana magana zuciyan shi na bashi cewa idan baiyi hankali
ba zai samu matsala daga mahaifiyar shi.

   Don haka dole ya
san yadda zai shawowa wanan lamarin tunkan yar mutane tazo azo a samu matsala a
tsakanin su.

    Gidan baida wani
girmane da ace shi wani mai wadatane da zai ginawa zahra gidanta daban ya
killance ta ya bata rayuwa mai inganci ya nuna mata kauna da soyayyan daya dade
yana mata a cikon zuciuashi.

    Zahra mace da ko
wani cikkaken namiji zaiyi fatan ya samu a rayuwanshi don ta kumshi abubuwa da
dama da ake son mace ta kasance dashi.

   Irin hakkuri da
sanin darajan mutum tausayi da kuma kula da na tare da ita uwa uba ga kyau ga
halita komai nata kamar ita ta zauna ta tsarawa kanta shi.

   Yasan baikai
matsayin da tun farko zai nuna kauna a gareta ba shiyasa ya fake da zumunta da
ita da yanzu ya zame mashi alheri a rayuwan.

    Yaso ace shi
wanine a yanzu da saiya gyara mata wuri har yafi hakan da yayi a yanzu din ko
yanzun ma zaiyi kokarim ganin ya killanceta ta yadda ba zata takura da yan
gidansu ba ko saka idon tsofafin shi.

   Yasan bata da
hayaniya kuma ba zataso yawan surutu ba ga zuwan kannin shi da mahaifiyan shi
yanzu gidan nasu ya koma masa wani iri da yawan hayaniyan da basu saba dashi ba
a baya.

    Allah cikin
ikonshi yana fita ubangidan shi ya kirashi ya bashi gudun mawar kudi bai dawo
gida ba ya shirya da maigina ya bada kudin komai da za a fara ja mashi katanga
a part dinshi.

   A tsare tsaren
hanne ta tsara zamuyi waliman mune a gidan wan mahaifin mu baba  Habu na mazon Allah kamar yadda mutane ke
mashi lakani da sunan.

   Ya kuma ji dadin
hakan da mukayi mai don su Aisha duk tsare tsaren su zasuyi shine a gidajen
kawayen mama masu fada a ji a cikin garin gusau din.

   Babu wani program
da suka kai gidajen ko wani dangi sai kuma hakan da mukayi din ya zama masu
wani magana da yaso ya jawo muna kace nace a tsakanin mu dasu.

   Inda mama keta
fadan cewa ai munafunci ne irin namu yasa muka kai event din gidan baba Abu din
wa zaije wanan gidan da baida tsari buki don dai bamu samu wurin yi bane muka
dahewa gidanshi ai kuma dama ai can ne daidai damu.

    Shiko baba habu
sai jin dadin hakan yakeyi duk inda ya hadu da yan uwa sai yace kai waga diyan
yar albarkata kunji wai gida zahra ta zaba zasuyi walima.

    Wagga diya Allah
ya rufa mata asiri duniya da lahira wadda tta nuna mu ubanantana Allah yasawa
aurenta albarka yasa ta gama da duniya lahiya.

    Yan uwa aka shiga
fadin maganganu kowa na fadin albarkacin bakinshi a kan mu hjy Asiyace kawar
mama da tazo daga Abuja tasa ayi odan abincin da za aci a wani hotel da zasuyi
muna duk abincin da za aci har na taron bukin da za ayi a fannin mu.

   Don haka saika
dauka cewa babu wani shiri ko tanadin da akeyi a namu fanin sai gulma ya tashi
ga mutane cewa ummah ta lafai bata komai tana jiran Abba yai mata komai.

    Alhalin kowa
yabawa kudin shagalinshi har fannin yan uwanshi saida ya basu nasu kudin da
zasuyi komai nasa ba tare da wani ya matsawa wani ba har aga laifin juna.

   Ta koma fadin cewa
ai kowa ummah bata gaiyata ba ga bukin don tasan cewa kunya zataji kai
maganganu dai marasa dadin ji gasu nan zuwa garemu mama tana sakewa gari ya
dauka.

 

Leave a Reply

Back to top button