Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 43

Sponsored Links

CHAPTER 43

Yanda ta cuƙwiƙuye masa riga tabaya har jikin su na gugan na junan su yayin da Ahmad yashiga wani irin yanayi mara misaltuwa dan ji yake kaman da gayya da saninta take masa hakan,amma saboda miskilanci irin tasa baka isa cewa ga halin da yake ciki ba.

“Aisha taho ki zauna muyi magana dake amma sai kin nutsu kin maida hankalinki jikin ki,girgiza mata kai tayi kana tace”a’a Anty hajiya dama kadai yake jira ya tafi alhali tunda yafurta hakan to kuwa aiwatarwa a gunsa abune mai sauki ban shirya gantalar da rayuwata ba haka kawai yamai sheni karamar bazawara da wani auren sa na wucin gadi kai ina,duk wanda yake da saka hannu cikin wannan abun naringa jaa masa Allah ya…saurin rufe mata baki yah faisal yayi be bari takarasa fadin abunda ke bakin ta ba.

Yana girgiza mata kansa alama karka sake cewa wani abu,kuka mai karfi yataso mata irin mai cin rannan tun daga ƙasa zuciyar ta tashiga rerawa jikinta har rawa yake,tasoma cewa”wayyo Allah Anna kin tafi kin barni a lokacin da nafi bukatarki kusa dani ni marainiya ce bansan rayuwar daɗi ba saina rufin asiri bansan mai duniya take ciki ba lokaci ɗaya farat ɗaya narasa mahaifiyata farin cikina shin tana rayene ko bata raye na tabbata da tana tare dani yanzu da hakan bata faru dani ba nayi rashin kafaɗa da zan daura kaina nafaɗa mata damuwa ta nayi rashin cinya da zan kwanta nayi kuka waye ze sharen hawayena wayyo Allah gani gareka bani da karfi bani da mataimaki sai kai ka taimakani ka kuɓutur dani daga zalumcin wannan bawa naka rintse idanunsa yayi da karfi yana mai dunƙulu hannun sa wani irin turin bakin cikin da zallah taƙaici yake taso masa har hucin sa da wani irin zafi yake fita.

Hajia ikilima ma kuwa jagwaf ta zube saman ɗaya daga cikin kugeran da sukama falonta nata ƙawanya tayi tashiga sharan ƙwallah,ganin haka yasa Aisha sakin Ahmad tazo ta zube gwiwa biyu gaban ta tana cewa”dan Allah anty hajia kiyi hakuri kidena zubda hawayenki kaina,ke tamkar uwace gareni hawayenki musibace gareni na yarda zan iya daukan komai amma banda wannan maganan auren na wucin gadi nan idan ko kema kika goyi da bayan yin hakan to wannan yana nufin rasa dukkan nin farin cikina ne.

Ahmad dake tsaye be juya ya kalle su ba,yayi ficewar sa yah faisal na biye dashi abaya.

“Boo wai meke faruwa ne?narasa gane kan wannan abun naku,naji kai kana kiran auren wucin gadi ita kuma tana kukan bata yarda ba wai me?

Numfashi daya gumsa a bakinsa ya fesar yana mai saka hannuwansa cikin gashin kansa yana yamutsawa idanun sa rintse ya datsa leɓansa na ƙasa da karfi kaman ze fudasu saboda ƙunci dayake ciki can kaman ba zeyi magana ba har yah faisal ya fidda tsammanin zaiyi magana sai kuma yace”nima kaina bansan abunda ke shirin faruwa da ni ba,tako ina ba sauƙi ɗan uwa.

Rana zafi inuwa ƙuna,inda nake tsammanin samun sassauci garesu suma kaga inda suka ɓulomun,dafashi yah faisal yayi yana cewa”boo kakara hakuri in shaa Allah zakaci riban hakuri da biyayya,daga haka yarakashi yashiga mota yatafi shi kuma yana mai tausayawa ɗan uwan nasa aure biyu lokaci daya kuma duk babu zaɓin ka aciki abun da ciwo amma idan kayi hakuri sai kaga alheri.

Alhaji sunusi yashiga tsaka mai wuya dan ba ƙananun ƙudi yasaka a wannan harkan ba,waya yake hankali tashi sai faɗi yake”mambila wai wani dan kasadan ne wanda bayason rayuwan sa yakeson wasa dashi?

A ɗaya ɓagaren naji wanda aka kira da mambila yana cewa”Alh gaskiya saide kayi hakuri dan koma wanene ba karamin tanadi yake dashi kanka ba,dan da alama be fara wasan ba sai da yashirya kuma duka cikin hukumanmu babu wani wanda yake da masaniya kansa,da alamade umurnine daga sama kuma kafin ya turo da kayan nan zuwa head quater saida duniya tasan da labarin nan kaga bamu da ikon yin komai akai idan akwai abunda zance maka befi nace ka tsagaita na ɗan wani lokaci ba.

Dan abu kazan uban nan yafaɗa da karfi yana baya baya kaman ze faɗi Allah yabashi ikon tsayuwa da ƙafafunsa,yanzu mambila kana nufin mutsaida komai saboda wannan banzan da be bayyana kansa ba?

“Kwarai kuwa Alh bakaji ance kaji tsoron abokin gabanka na ɓoye ba,dolene mu canza tsarin komai idan ma yana bibiyar komai namune to yanzu zamu canza tsarin komai duk wani jadawalin na farko zamu kansale.

*****
Rarrashin duniya nan hajia ikilima tayi amma babu wani canji wajen Aisha dan sai cewa take saboda anga ni marainiya ce akaimun haka ai da iyayenta na tare da ita ne ko banza zasu bukaci jin ra’ayinta.

Karshe saida hajia ikilima ta ɗauki waya takira Ammin tana dagawa ko gaisawa bata bari sunyi ba tace”yaya akwai matsala?

Miƙewa tsaye hajia ma’arufa tayi tanufi hanyan ɗaki dan tana tarene da ƙawayen hajiya mariyah da suka zo jere lokacin,saida tashiga ɗaki yarufe kofa harda murza key sannan tace”matsala ikilma ta mefa?

Nan Anty hajiya takwashe komai daya faru ta sanarwa yayatata ta kara da cewa”yanzu haka aikin rarrashi nake amma ko kadan taƙi saurarata bansan ya zanyi ba,Ahmad yaxo duk ya dagula komai tafaɗa kaman zatayi kuka.

Dafe goshinta tayi tana mai cewa”dama fitan da yayi ɗazun gidan naki yaje?barshi ze zone yasa meni yaro besan ana masa gata ba,hmmm”kede yaya bari kawai wai har cewa fa yayi zamu aura masa jaririya ko rainon ta zeyi.

Dan dariya hajia ma’arufa tayi kana tace”ze gane rainonta zeyi ba zai taɓa sanin gata muka masa ba shi da uban sa ba sai nan gaba,kinsan Allah ikilima baki bani bashin rantsuwa ba amma kwata kwata jinake ban yarda da wannan haɗin auren na Ahmad da ɗiyar Alh sunusi ba,gani nake kaman da wata a ƙasa wallahi shisa nadage kai da fata saida aka daura da Aisha sannan naɗanji dama dama ko ba komai zata zamewa ɗana garkuwa haka nakeji a raina.

“Kwarai kuwa yaya haka,amma ya akai mutanen naki suka canza shawara suka yarda da tarewar ɗiyarsu bayan da sunce saide Ahmad ya tare gidan su?”Allah masani ikilima banace ba,ko sunga kaman zargi ze shiga tsanine suka canza taku oho kin kuma san halin ɗanki tunda ya tirje bazashi ba to bazashin bane dan haka sukai da uban inaga koshi sa suka canza tsarin nasu mude Allah muka rika mutum ko tashi sama yake saboda tsafi da yardan Allah ba abunda ze samemu,na cikaki da surutu jeki lallaɓa mun ɗiya da zaran ɓakin nan sun tafi zaki ganni.

“Tom yaya sai kin dawoɗin sukai sallama koda ta waiga taga wayam ba Aisha dake zaune dan haka hankali tashe ta nufi ɗakin su nan ta cammata ta haɗa kai da gwiwa sai kuka take.

Zama tayi kusa da ita tasaka hannu ta ɗago da fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tace”sai kika tunomun da yayata sanda aka ɗaua mata aure da mijinta wato mahaifin su Ahmad kinsan yanda tayi kuwa?

Bata jirayi amsa gunta ba taci gaba ta cewa”haka tasaka kakarmu gaba da kuka da bori kamande yanda kikayi ɗin nan karshe wasu daga cikin ƴan uwa suka yanke shawaran kawai ya sauwake mata tunda bata ra’ayin sa,sai wani dattijo yace ku kira ita yarinyar muji ta bakinta kafin a yanke hukunci.

Koda yaya tazo da wannan dattijon tsohon kakannamu ya tambayeta kaman haka”ma’arufa shin wannan miji naki bayi miki ba a warware auren a maida gawani wanda kike so kukuwa?

Buɗan bakin yaya sai cewa tayi cike da ƙuruciya nide gaski Alhaji babba bawai shiɗinne beyi mun ba kawai ina kukane idan natuna wannan ƙatuwar tumbi nasa nace wa ƙawayena wannan ne mijina aisai sumun dariya karshe suma idan ba sa’a akaci ba susaka shi waka a dandali ai Aisha batasan sanda da fashe da dariya ba harda riƙe ciki……

 

 

Leave a Reply

Back to top button