Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 20

Sponsored Links

Chapter 20

“Oga mungama shirya komai na barinka wajen nan a daren yau,muryar gaja ne ya katse masa magana da yake,wani ƙayatattaccen murmushi yayi yana kallon gaja yace”ya kai da sauran karnukan farautan nasu?
Wannan tambaya ta bawa gaja dariya saida yayi mai isar sa sannan ya tsagaita yace”sai oga ishaq ai komai ya kammala nan da awa guda zakabar zaman nan ina maka fatan nasara dakuma fatan saduwa da iyalanka dan inaji a raina kun kusa haɗawa da juna bansan abunda yasaba amma akwai wata yarinya da nake gani a duk sanda zan ganta sai naji kaman tanada alaƙa da kai.

Da sauri daddy ishaq yace”ya kaman ninta suke kuma aina zan sameta?sosa kai gaja yayi yace”gaskiya oga bansan inda take ba,amma ina yawan ganinta a A&b travel kasan wajen ranan nacema na ɗan Alhaji badamasi ne mai suna Ahmad kuma shi alh sunusi yakeson bashi auren ɗiyarsa,
To cikin wajen a yanda bincike na yanuna bayan motocin safara da suke dashi akwai wajen ɗinki saboda shahara dakuma gwarewar ma’aikatan wajen kayansu order ake garigari harma da kasashen ƙetare ina kyautata zaton wannan yarinya a wajen take,sannan akwai informer da muke da iya awajen zamu sami dukkan bayane da muke bukata wajenta saide har yanzu tace yarinyar bata sake da ita sosai ba,dan acewar ta kamar bata da sabo da mutane.

Gwaron numfashi daddy ishaq ya sauke yace”ya batun wannan flash din?
Mika mishi gaja yayi da kuma cemasa duk wani ƙarin bayanin da kake bukata zaka samu cikin sa oga sannan duk sanda wani abu ya shige maka duhu kiyi alart ɗina ta turamun da sakon lambobi a hargitse,hannu daddy ishaq ya mika masa sukai musabaha cike da jin daɗi yace”in sha Allah kuma kaima zanyi iya yina dan ganin nasama maka da duk wasu bayane da kake bukata daga gareni.

Alhaji shehu tunda ya daura idon sa akan aisha yakasa samun tsuwa da sukuni zuciyar sa da zaran ya kwanta ita yake gani ya tabbata ya kamu da soyayyarta mai karfi,ɓangaren fadila kuwa komai yana tafiya mata yanda take so,tasamu yanda takeso rayuwa ya canza mata yanda takeso tana juya naira yanda taso,gashi ba abunda suka nema a rayuwarsu suka rasa.

Tasaka an rushe musu gidan ana yi musu ginin zamani ginin bulo da bulo yanda tasaki kuɗi aiki ake ba dare ba rana cikin ƙwana biyar har antada katangar gidan dakuma ɗaki ciki da falo da bayi na mamatar an fanti yanxu haka ɓangaren babanta da na yayunta maza biyu ake gini dan dama gidan nasu yana da girma,zaune suke da mamarta sun baje sunacin shawarma suna korawa da ruwan lemo mai sanyi mama rabi ta kalli ɗiyar tata cike da kulawa da so da kauna tace”shegiya naira masu gidan rana,yanzu kiga rayuwarmu ta canza lokaci guda waima fadila wani kalan sana’a wannan Alhajin keyi dan tamusu karyar Alhaji shehu shiya ɗauki nauyin gina musu gida kafin ayi maganar auren su, Allah de yasa ba ɗan yankan kai bane.

Ɗan harararta fadila tayi a ƙaikace sai kuma tace”yankan kai kuma mama ai rabin kuɗin nawane dan nima sana’a nake nema nake tuƙuru saboda huce haushin talauci da mukai abaya,yanzu kuma lokaci yayi da zamuji daɗi muma musakata mu wataya cikin daula”fadila kaji tsoron gamuwarki da Allah suka tsinkayo muryan babanta daga baki ƙofan falo,ki guji duniya da abunda ke cikin ta dan wannan arziki da kikayi lokaci ɗaya kin saka mutane ana zargin ko kuɗin jini…katse shi mama tayi da cewa”haba malam bantaɓa sanin baka da hankali ba sai yau,idan baka gode mata ba ai bata cancanci haka daga gareka ba,shikenan ba dama mutum yayi abun kansa sai ansa masaka ma ido,mutum daya sami canji kaɗan a rayuwarsa sai sunsan abunda sukace akan ka kawai baƙin ciki ake dan anga munsamu canji a rayuwa malam toshe kunnenka zakayi gajin irin waƴan maganganun mutanen.

So kawai mutane suke su ringa kallon mu jiya i yau garin tuwo na gagaran mu haka sukeson ganin mu muna yawon neman aikatau kororo kororo ana zaginmu,shiru yayi mata yana sauraronta dama gwanace wajen masifa da son abun duniya dan tun can idan tafara surfa masifanta a gidan ba mai kulata,yanzu ma saida takai ayaa sannan malam inuwa wato mahaifin su fadila ya sauke gauron numfashi ya kalleta cike da ɓacin rai yace”kingama?

Wannan tambaya da yayi mata ya bata haushi dan haka a hasale ta hau bambamin bala’i ai hasada yake wa ƴarta dan kawai ita Allah ya ɗaukaka cikin su so kawai yake yarinka ganin su cikin ɓakin talauci idan ba haka ba,ya kwantar da hankali yaci arziki amma kullum mutum kana fama da wankin hula yarinya Allah yahure mata bazaka sanya albarka a abun ba,yanzu duba ko a iya gyaran gidan nan ta tsaya ai abun burgewa da tunƙahone agareka ace ɗiyarka Allah ya azurta tas….wani irin wawan tsawa daya daka mata hakan yasa tayi shiru tana ta muzurai nunasu yayi da yatsaya yace”ni ko farko banyi farin cikin gyara mun gida da sukazo mun da shi ita da wawan mutumin can bari kiji rabi Allah ya rufamun asiri bazaki nemi tonamun ba,ya kalli fadila yace kice masu gyaran nan su tattara subarmun gida,shi arziki nufine na Allah idan yayi zakayi to ba wanda ya isa hanawa,haka idan bebaka ba ba wanda ya isa yabaka duk duniya.

A kullum ina godewa Allah daya rufamun asiri keda kike ganin wannan abun burgewane a wajenki kuje can kukarata kar wanda yasake cemun komai gidade nawani ba uban kowa ya saimun ba,bara kiji rabi duk wanda ya hau motan ƙwaɗayi a tashar wulakanci za sauke shi yana kaiwa nan yayi ficewar sa a gidan,kuka fadila ta saka ganin kaman mahaifinta yanason kawo mata cikas a fasowa gari da tasomayi.

Ahmad zazzaune suke bayan sun gama cin abincin dare hira suke da ƴan uwan shi cike da raha meera autar ammi ta kalle shi tace”yah Ahmad ranan munga wasu dogin riguwa a status ɗin yah khalid ya daura masu masifan kyau”shine kikeson kalansa ko?yakare maganan yana jan hancinta dariya tayi tace”wallahi yah ahmad kaman kasani kuwa fadwa ta amshe da cewa”kuma kinji yah khalid yace wannan kayan bana sayarwa ko kyauta dasu bani saboda….kinga ruwafa mutane baki da shegen surutun tsiya faɗi ba tambayeta ba,
Tura baki tayi tana magana ƙasa ƙasa shide ahmad shiru yayi be sake bi takan zancen nasu ba.

Alhaji badamasi ne yashigo falon rai aɓace sannu da zuwa yaran sukai masa amsa musu yayi ciki ciki ya ƙurawa ahmad ido shiko ahmad ƙasa yayi da kansa kaman ma besan shi mahaifinasu ke kallo ba alhali kuwa yana yana ankare da irin kallon da yake masa yanama autar ammi wasa hakan yasake ƙular dashi koda ammi tace”Alh sannu da zuwa ga ruwan wanka can na haɗa maka muje kayi sannan kaci abinci.

Harara ya watsa mata yace”ai dole kice nayi wanka tunda gani kifi sarki ruwa shi wannan ya maisheni mahaukaci ina magana yayi buris dani,sannan ke kuma kizo kina wani zancen wanka to ba za’ayi wankan ba,yafaɗa a hasale”Allah yabaka hakuri alh”nabi hakurin da gudu nace nabi hakurin da gudu shiru ammi tayi bata sakeyi masa magana ba.

Fadwa da meera kuwa miƙewa sukai suka wuce dakin su,sai sannan ahmad ya dago ya kalli ammi data dauke kanta tana kallon tv shiko alh badamasi tsaye yake ƙiƙam kaman wanda aka dasa miƙewa yayi yace”ammi sai da safe ko,kallon sa tayi da murmushi a saman fuskarta tace”ahmad harzaka tafi?to Allah yatashe mu lafiya.

Ganin da gaske wucewa zeyi yasa alh badamasi daka masa tsawa yana cewa”oh ga ɗan iskanan kowa sai guduwa yabarni dan kun maisheni mahaukaci ko?to maxa koma ka zauna.

Komawa ahmad yayi ya zauna”saboda baka ɗaukeni bakin komai ba baka ganin girmana ɗazu da zan fita nace kaje kasami wannan yarinya ku tattauna shine kaƙi tafiya ita mace ma tayi biyayya ta yarda da auren ka sai kaine zaka nemi watsamun ƙasa a ido ko.
“Au dama yanzu duk wannan ƙucin ran da kake sabida ahmad beje gun basma ba kake yinsa to Allah ya kyauta daga haka tamiƙe tsaye tabar falon rakata da ido yayi shi kaɗai yasan halin da ze shiga idan tayi fushi kafin ta sauko.

Sake yin kasa ahmad yayi da kansa cikin kwantar da murya yace”haba Alh mai yasa kake hakane gashi yanzu kasa ammi tayi fushi sannan idan zanje wahen yarinya zance ai baku iyaye zaku saka mana rana da lokacin haɗuwa ba,sai kace ƴan 80c ai yanzu zamani yanza duk sanda mukai zamu haɗu bada saninku ba zamu haɗu kumama ni yanzu aiyuka sunsha mun kai bana tsamanin zanje cikin yan kwanakin nan saide namusu zuwan bazata,har yamiƙe sai kuma yace an Alh gaskiya koda zan aurin yarinyar nan da sharaɗin nima zaka bani nawa daman dan auro wacce nakeso ta kwantamun arai zatamun biyayya kuma zata zauna da mahaifiyata ta ringa taimaka mata da ayyukan gida,daga haka be bawa alh badamasi daman cewa wani abu ba yayi shigewar sa,bayan ya shige daɓas alh badamasi ya zube saman ɗaya daga cikin kugerun falon yana mai dafe kansa da tuna yanda sukai yarjejeniya da alh sunusi daga ɗiyar sa Ahmad ba zaikara wani auren ba,sai gashi ba aje gayin auren ƴar tashi bama ahmad ya bijiro masa da zance karin aure take wani irin zufa ta karyo masa yama rasa meke masa daɗi

Leave a Reply

Back to top button