Auren Wucin Gadi Hausa NovelHausa Novels

Auren Wucin Gadi 53

Sponsored Links

CHAPTER 53

 

“To aiga irin tanan ana baka kana roƙa kai zaka iya batawa da kowa akansa dan farin cikin sa amma shikuma baze iya batawa dako ɗiyar da ya haifaba saboda farin cikinta na sama da kowa awajen sa,sai kakira Ahmad ɗin kaji ta bakin sa amma inde a haka zaku tafi bana tunanin wannan aure da kukeson kullawa zeyi tasiri dan shi Ahmad mutumne mai kafiya da tsayuwa kan magana ɗaya shikuma Alhaji sunusi mutumne daya fifita bukatarsa saman komai a duniya kai kuma bazaka iya ƙetare maganan shi ba kaga kuwa Ahmad dinne ze sha bakar wahala dan wannan yarinya bana tunanin ko ruwan zafi ta iya girkawa.

 

Ganin tagama maganan tana shirin miƙewa”koma ki zauna ina kuma zaki ikilima ai sai kitsaya ki saurareni tunda nima danake babba sama da ke natsaya na saurari ta bakinki,kawai de zance dake inde kisan da bakin ki ko dana ƴar uwaki Ahmad yasa Ahmad yin haka wallahi kuyi gaggawan cemasa ya janye daga kudirinsa yakuma dawo gida in kuma yayi wasa wallahi insa yau dinnan adaura masa aure da basma kowama ya huta.

 

Ƴar dariya Anty hajia tayi tace”yayah amma kanada abun dariya yo idan aure zaka daurawa Ahmad sai kazo ka nemi fada mana yo mume namu ciki,bakaga muda mukasan zafinsa dakuma sanin abunda ze faranta masa ai sai ji kawai kayi mundaura masa aure da wacce tafi dacewa da rayuwarsa wacce kai da kanka sai kazo kana alfahari da zamowarta surukarka.

 

“Oh ta haka kula ɓulo to bari kiji wallahi wallahi dande kun saka malam cikine badan haka ba da tuni nasaka ya rattaɓa mata saki ai ni ku yanzu wannan auren ban ɗaukesa aure ba auren wucin gadi kinsan abunda ake nufi da na wucin gadi to haka na daukesa lokaci ƙanƙani nake jira”Antyn yara aka kira daga bayansu tare suka juya jin muryar Ammi yasa Alh badamasi yin kicin kicin da fuska itama haɗe fuskarta tayi ba alamun wasa tace zoki wuce ki tafi gida mayi waya anjima.

 

HAJIA MARIYA

Ganin kukan na basma bana karewa bane tashiga rarrashinta harta samu ta shawo kanta tayi shiru ta faɗa mata damuwarta,murmushi tayi ta kamo hannun ta tariƙe tace”basma kefa ba yarinya bace karama haryanzu da komai sai daddynki yashige miki gaba sannan zaki samu.

 

Keko ƴar kissarnan ta ƴan matan zamani baki iya ba kice komai sai da izza zaki mallakeshi kisani wani abun karfin izza data mulki kuɗinki shi zesa ki mallakesa ba, wani abun saida ƙaskan da kai sannan ne ze kaiki ga samun abunda kikeso.

 

Yanzu duba kigani da kinje masa da lallami da tausassan kalma da yanzu kinsami biyan bukata amma kinje kinyi masa wannan haukan naki taya ze saurara miki shin baki taɓa jin shikansa daddyn naki yana faɗi a harka ta kasuwanci babu sani ba sabo ba,yanzu gashi kinge kinsaka daddynki ciki ƙila yace koda karfin kuɗi saiya samo miki wannan riga saboda farin cikin ki amma shi Ahmad ɗin naki kinɓata masa…..shiru tayi tana sauraron mummyn tata a can karkashin ranta kuwa tunani take yaushe mummynta tazama haka take magana cikin sanyi.

 

Ganin kaman tana tunani yasa mummynta dan tabata kamanko tasan abunda take magana aranta tace”kinga bar wahalar da kanki sai kinsan komai kibar komai yanda kika gansa yanzu de tashi kishaga kisamu kiyi wanka ki kira Ahmad ɗin a waya ƙila yasauko daga fushin da yayi ki kalallamesa karkuma ki dauko masa zance rigan mude samu yasauko da fushin tukunna musan abunyi da haka tasamu ta korata ɗaki ita kuma ta zauna zaman jiran Alhajin nata.

 

 

Aisha koda tashiga ciki wanka tasamu tayi hankali kwance,tafito bedroom dinta daure da towel saida ta tsane danshin ruwan jikinta sannan ta zauna zaman shafa jikinta da lotion masu kyau da daɗin kamshi tana gama shafa man ta jawo turaruka ta feshe jikinta dashi light makeup tayi sai kawai taji aranta ranason saka wannan rigan kai sai ta jawo abarta tasa tashiga juyi a gaban mirrow ita kaɗai sa sakin murmushi take kawai sai dauko wayanta da kasheta ta ajiye tun kwanaki takunna saida ta gama searching sannan tashiga camera tasoma haska kanta da hotuna saida tayi mai isarta sannan ta tsagaita abunda bata taɓa yiba daura hoto a media shine yau tayi na musamman amma a IG dan nan sukafi ɗaura tallan kayansu idan sunyi sabbin styles imoji tasa daidai kan fuskarta sannan tayi rubutu kaman haka dayaja hankulan mutane musamman matasa ƴan uwanta masu sana’ar dinki.

 

 

_kowa da kudinka saida rabonka bawai ina magana kan kaina bane a’a ina maganane kan wannan riga dake jikina matsayina na ɗiyar da nakowa ba ban isa na mallaki wannan kayan ba,Abu na Allah wai budurwa da jika kasancewa ta telah sai gashi na dinka abata na nasaka ina alfahari da sana’ata ta telah muba abun rainawa bane kaman yanda wasunku suka daukemu neman gumin mu muke bawai roƙo ko bara muke ba,kaman yanda wasunku suke ɗaukan mu kawai sukawo muna kaya mu ɗika musu subamu kuɗinmu idan kuma akasamu akasi rashin gama musu ɗinkinsu akan lokaci su rufe idonsu suci mana mutunci basa tunanin gobe ma zamu sake gamuwa sude ganin su ai kuɗinsu ke aiki dan haka bamu da saura mutunci awajen su tunda kudi suke biyanmu.

Tellah ba ƙasƙantacce bane mu teloli jajirtattune jinjina ga telolin da ke faɗin duniya baki ɗaya dan ko shugaban ƙasa ayau da bazarmu yake taka rawa dan sai mundika sannan ze saka tufafin da zefiti jama’a suyaba na jinjina mana matasa ƴan uwana kumu riƙe sana’armu hannu bibiyu watarana ze kaimu inda bamuyi zato ko tsammani ba mukasance masu cika alkawari sabida girmanta_ 👏🏽

 

Tana turawa sai kawai kira yashiga wayan ta ƙirgijinta ne yashiga lugude yana dukan tara tara dan yafi karfin uku uku bata taɓa jin faduwar gaba irin haka ba,idan yakirata koda yaushe takan tsimayi kiransa cike da zumuɗi take ɗaga kiran har Allah Allah take lokacin kiransa yayi susha hira amma yau itace rana ta farko da taji hakan a ranta kuma ta tabbata ba komai yasa tashiga wannan yanayin ba sai girma igiyan auren mutumin da bema dauki abun dawata daraja ba akanta wata ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauke daidai kiran ya katse wani kiran yasake shiga.

 

Ƙuntum bala tayi wajen dauka wayan tayi takara a kunne batare da tayi sallama ba,ajiyar zuciya taji yasauke mai karfi cikin sanyi murya kaman na wanda bashi da lafiya yafurta”so keki kikasheni ko hamaira?

 

Batasan sanda kuka ya kubce mata ba,kawai sai ta fashe masa da kuka jin kukanta yasa hankalinsa ya dugunzuma wajen tashi ji yake kaman yajawota tacikin wayan yabata hakuri”Ana asif ya habibi shine kawai abunda take iya faɗi cikin kuka.

 

 

Kusan minti goma tadauka tana kuka shi kuma yana sauraronta,abu biyu takewa kuka na farko mahaifiyarta da har yau bata da yaƙinin shin tana rayene ko kuwa wane hali take ciki shin tana cikin ƙoshin lafiya ko tana halin jinya shin tama samu taci abinci ko tana can tana bara su suna zaune anan hankalin su kwance duk daren duniya sai tayi kukan rashinta atare dasu,abu na biyu kuma shine Suhail dole ta fito ta faɗa masa gaskiya bazata rufesa ba ko dan darajan soyayyar gaskiya dayake mata.

 

Cikin rawan murya tace”Suhail kai hakuri dan Allah badan halina ba banyi hakan dan na ƙona maka rai ba,saide inaso matsayinka na musulmi wanda yayi imani da Allah da kuma kaddara maikyau ko akasinsa Suhail kaine wanda nafara so tun bansan menene so ba,inaso kamun alkawarin duk abunda na faɗa maka zaka daukesa matsayin kaddaranmu bazaka kuma yimun mummunan fassara ba”cike da zaƙowa yace nayi duk da wani sashin na zuciyarsa tana faɗa masa wani abu abu mara daɗi amma haka ya daure yace yayi.

 

 

Dakyar ta aro jarumta tasakawa kanta tasan wannan itace hanya daya dazata faɗa masa gaskiya kafin yaji abakin wani yadauketa mayaudariya”inaso ka auri ƴar uwarka Suhaima dan itace ta dace dakai.

 

Wani irin miƙewa yayi tsaye dayajawo hankulan iyayensa da ƴan uwansa duka dake zaune a falon dan tattauna ta yanda zasu ɓullowa abun ganan suhaima ta kusan kamuwa da ciwo zuciya sanadin sonda take masa shi ance ya hakura a aura masa ƴar uwarsa yanzu in yaso daga baya suje nigeria neman masa auren wacce yakeso yaƙi yace shifa sai idan ansoma nema masa auren Aishan in yaso ayi na suhaima daga baya.

 

Ita kuma suhaima cewa tayi inde ze aureta koda na wucin gadine ta yarda muddin zata amsa sunan matar sa yaje ko Aisha uku ze auro ya auro.

 

Jikinsa sai kyarma yake kaman mazari besan sanda ya faɗa saman kugera daya tashi ba,umminsa ce ta karɓi wayan daga hannun sa tasaka ta hands free tayanda kowa zeji.

 

“Habibi kai ɗin ka kasance masoyin gaskiya dakai nake kwana dakai nake tashi acikin raina tunaninka betaɓa gushewa acikin raina kodana na diƙiƙa ɗayane ba,saide bazan yaudare ka nakuma yaudari kaina mufaɗa cikin fushin ubangiji saboda son zuciya ba.

 

An dauran aure da waninka bansan ya ze karɓeni matsayin mata ba,shin zan dace da auren koko?

 

Nide nayi bibiyane nasan kuma duk wanda yama iyayensa biyayya Allah ze dubi lamuransa,Anta mahbub da’iman kukane yaci karfinta ta yanda baxata iyayin wani maganan ba sai sautin kukanta dake karaɗe kunnuwan su tsit kakejin falon shikansa suhail ba zakasan awani yanayi yake ciki ba saboda kasa dayayi da kansa,suhaima ce ta rarrafa tazo ta faɗa jikin sa tasaki kuka mai karfi tana cewa”akhi kaje kazo da ita itaɗin masoyayiyar gaskiyace hakiƙa ni naza maison kaina nasan Aisha ta gujeka ne kawai sabida goranta mata launin fata dakuma kiranta da kwaɗayayya mara asali da nayi yasa ta yanke wannan hukunci,tabbas ita ɗin mai zuciyar zinarice tunda bata taɓa faɗama irin cin mutunci da zaginta danakeyi a waya ba,bayan sakon txt dake rubutawa na cin mutunci da tozarci danake tura mata bata taɓa maidamun da amsa koda sau daƴane ba nasan hakkin wannan abunda namata shike bibiyata Allah yajifa mun soyayyarka acikin zuciyata gashi tana bara zana ga rayuwata wacce na raina nake ganin nafita dakomai ita tayi nasaran mallakan zuciyarka dan allah akhi alfarma ɗaya zakamun koda na rasa rayuwata kazamo….sauri rufe mata bakinta yayi da tafin hannunta yana girgiza mata kansa dagowa yayi da rinan nun idanunsa dasuka kaɗa sukai jajir dasu fuskar nan tasa ita tayi jaa sabida tashin hankali dayake ciki,miƙewa yayi batare da yace komai ba,yayi hanyan ɗakin sa sai juwa dake kokarin kadashi saurin miƙewa ummi tayi dan bin bayansa amma sai Abbiy ya katse mata hanzari yace”barshi yana bukatar keɓe kansa ku barshi ya huta,da haka taron ya watse sai suhaima da aka bari falo tana rizgar kuka da kiran duka lefinta ne ita tajawo Aisha ta guji suhail tayi da tasanin bin shawaran kawaye datayi sosai.

 

ALHAJI SUNUSI

Sai gabda kiran sallar magariba sannan yazo gida koda yazo ɗakinsa yawuce direct saide yana bude kofan ɗakin wani kamshi mai daɗi yabugi hancin sa,lumshe idonsa yayi dan shifa gani yake tunda yake a rayuwarsa betaɓa jin kamshin turaren daya tafi dashi irin wannan ba.

 

Haj mariya dake laɓe bayan labule tafito cikin takun katsaita tazo ta rugumesa tabaya take yaji wani irin azabebben feeling wanda betaɓe jinsa ba akanta rugumeta shima yayi nan labarin yasha bamban nima mai dauko muku rahoto sai fitowa nayi naja musu ƙofa dan fa abun na manyane.

 

Ahmad

Baccin sa sha sai karfe biyar ɗin yamma yasamu daman farkawa da azaban ciwon kai lallaɓawa yayi yafaɗa toilet wanka yayi tare da dauro alwala yazo ya gabatar da sallan la’asar da besamu yayi ba karamar wayansa yaɗauka wanda bakowa keda wannan lamba ba yakira Ammin sa lokacin tana ɗaki zaune ta rabka tagumj hannu bibiyu ita tarasa meke damun mijinta kowa nason ganin farin ciki da walwalan ƴaƴansa amma banda shi,gashi yanzu yaɓatamun rai amma bemasan yayi ba yanzu haka jira yake naje nabasa hakuri wallahi wannan karon baxan bada hakuri ba tunda kan wannan mutumin ne.

 

Wayanta dake ringing ne ya katse mata hanzari dagawa tayi batare da tasan wanda ke kan layin ba”Assalamu alaikum Ammi yafurta cikin sanyi murya.

 

Wani irin dadine ya ziyarci xuciyar ta har hakan ya bayyana a muryarta amsa masa tayi da”wa’alaikum salam Ahmad ina kashiga ne duk katamun da hankali.

 

“Ammi kwantar da hankalinki tafiyace ta kamani na gaggawa zanyi sati kafin naxo”Allah yakamaku ashe keke zuga yaron nan yake mun iya shegen da yaga dama bani shi bani shi yafada yana warce wayan daga hannun Ammin saide kafinma yakai wayan kunnesa Ahmad yariga daya kasheta baki ɗaya tunda yaji muryarsa yakuma daura damarar yakan Alhaji sunusi da fiddashi cikin rayuwr mahaifin nashi……ja’irin yaro yakashe wayan yafaɗo rike da wayan a hannun sa.

 

Leave a Reply

Back to top button