Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 41

Sponsored Links

 

SAKAYYA

 

41

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

 

_Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

 

 

🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

 

 

Araunane tace.

“Ummi dukana fa yake sawa ayitayi kawai dan mugunta”.

Cikin sassauta murya Ummi tace.

“Khausar Rayuwar makaranta da ban, sannan rayuwar da zakuyi yanzu shima daban bazai da keki ba”.

Kai ta girgiza still Hawaye na bin kuncinta tace.

“Wallahi Ummi mugunune kobai dakeni ba, zai ta cin zalina, nasani koma mene zaimi. Allah zai saka min zan jure domin cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke cike da ɗan murmushi tace.

“Kada ki manta Shifa ba jahili bane yana da ilimi kuma shi Modibbo mutum ne da yasan darajar ɗan Adam. dan haka ki kwantar da hankalin ki, kinji ki daina jin tsoron dubi yanda baki ɗaya kika rame nasan harda maganar nan yasa kika rame to ki cire abin ki sa a ranki abokin ne yanzu bawai malaminki ba”.

 

Numfashi Asma’u dake fitowa ta fesar tace.

“Ummi haka jiya ma tayi ta kuka da daddare nima tayi ta sani kuka”.

Still tana jikin Ummi tace.

“Kada kiyi kuka ki saki ranki rayuwar inci zakije kiyi.

ki fara shirye-shiryen ki da zuciya ɗaya Insha Allah zakiyi al’fahari da wannan auren”.

Cikin tura baki tace.

“Ummi ni kuma wani shirye-shirye zan fara”.

Ɗan murmushi Ummi tayi kana tace.

“To ai dole kiyi shiri Khausar dudu yanzu saura kwana gomane dama abinda zai kaimu gidan Abban Jameel kenan”.

 

Zare ido Khausar tayi tare da dafe ƙirjinta tace.

“Kwana goma kuma Ummi da sauri haka dama dagaske ne?”.

Cikin murmushi Ummi tace.

“Dama da wasa kika ɗauka ne Khausar?”.

Kai ta girgiza tace.

“Bada wasa na faɗa ba Ummi amma kuma ai da anbari sai na gama karatuna”.

Ajiyar zuciya Ummi ta sauke tare da riƙe tafin hannunta tace.

“Karatu zakiyi agidan mijinki Khausar kada kiji tsoro kinji ko munyi magana ma da Mommy ki kafin ki iso, akwai wasu kayan turarukan wuta dasu Humra da kullaca, da dai wasu abubuwa da na saya miki  a wurin AYSHA ALIYU GARKUWA, in sha Allah nanda kwana biyu zata gama haɗa miki kayan zasu taho daga Adamawa, tam ce ta gama komai dahuwar kazane bata gama da kuma zuciyar farin rago su sabida da rubutu ake haɗasu”.

Shiru Khausar tayi batare da tace Uffan ba, sabida Allah ya sani batayi zaton da gaggawa haka za’ayi abinba.

cikin dabara Ummi ta riƙa kwantar mata da hankali tana mata nasiyya sai da taga ta nutsu kafin ta Miƙe da nufin shiga ɗakin innayi ta kirata su tafi.

Sai kuma ta gyara mayafinta juyowa jin Khausar na cewa.

“Ina yini”.

Murmushi tayi ganin innayi take gaisarwa, ita ma Innayin murmushi tayi ganin yadda Khausar ɗin ta sunkuyar da kanta.

Cikin kula da kauna tace.

“Lafiya lau kishiya ya gida”.

Guntun murmushi dake iya sama lebe Khausar tayi tare da miƙe ta kama hannun Asma’u suka nufi kitchen.

Ummi kuwa ƴar dariya tayi tare da cewa.

“Yauwa Innayi tunda kin fito tafi ko”.

Gyara mayafi Innayi tayi tare da cewa.

“Eh muje”. Nan suka fice suka tafi gidan Abban Jameel a sabuwar motar da ya sayawa  Ummi.

 

Asma’u da Khausar  kuwa suka ci-gaba da hiransu.

 

Suna na isa gidan Abban ta samu Malam Arɗo bayan sun gaisa Malam Arɗo yace.

“Toh jiya da daddare Lamiɗo ya kirani yace biki za’a haɗa dana ƴar wajensa kuma sunce Jumma’a na sama nema suke so aɗaura auren kunga yau saura kwana takwas nema, toh yace za ahaɗa dana Khausar”.

Jinjina kai innayi keyi cike da gamsuwa Malam Arɗo ya cigaba da cewa. “Sannan mun gama tattaunawa da Abban Jameel akan ayi kawai agama tunda dama Jameelu yayi ta jaddadawa cewa ayi ƙoƙari ayi shi cikin ƙanƙanin lokaci”.

Gyara zama Ummi tayi kana tace.

“Sosai ma ayi kokari ayi haka shiya dace”.

Gyara zama Malam Arɗo yayi kana yace .

“Sannan Alh Bashir yace kada ayi masa batun Auren”.

Kai Ummi ta gyaɗa cikin gamsuwa, shi kuwa Abban Jameel gyaran murya yayi tare da cewa.

“Innayi kada a faɗa masa fa, dan so nake muyi mishi ba zata”.

Cikin gamsuwa Innayi ta jinjina kai tare da cewa.

“Ai kuwa bazata kam suna da yawa kuma ɗin kanku akwai bazatar da zan muku.

Tunda in an ɗaura auren kai mishi ita za’ayi ko?”.

Da sauri Abba yace.

“Ni zan kai mishi ita”.

Murmushi Innayi tayi tare da cewa.

“A’a kada ka damu a gayawa dangin amarya su shirya yan rakiyar amarya da basu gaza goma”.

Da sauri Ummi ta juyo ta kalleta tare da cewa.

“A’a Innayi bafa ƙasar nan bane, har Marocco nefa,  ya za’ayi ace har mutun goma ai ɗawainiyar zatayi yawa, wurin sauƙesu ma ai jidali ne”.

Cikin sauri Malam Arɗo yace sosai ma kuwa.

Abba kuwa ido kawai ya zuba musu.

Ita kuwa innayi gyara zama tayi cike da yaƙini da kuma tabbaci tace.

“Kada ki damu Ummin Jameel, ai tuwon girma miyansa nama, kuma in dai masauƙine koda Gambulan baki ɗaya zamuje bazata rasa masauƙiba. Kana kema zakije Asma’u, Abban Jameel Malam Arɗo, dama Lamiɗon kansa zaije”.

Murmushi mai cike da nazari Abban Jameel yayi tare da tuno abubuwan da Jameel ya gaya mishi akan tarihin Modibbo da yace Innayi ta bashi.

Cikin gamsuwa yace.

Kada ki damu Fatima a gayawa mahaifiyar Khausar a samu mutun goma daga gefen dangin kausar na uwa da uba da ni kuwa zan gayawa Lamiɗo”.

Kai kawai Ummi ta iya gyaɗa musu, domin abin ya bata mmki tunda Modibbo fa ya gaya mata kuɗin tickets insa na business class  1,303,000  suku tum toh fisa bilillahi wannan kudi ai yawa garesu ace kusan mutun goma.

Jin Malam Arɗo yace.

“Ai akwai economic tickets, kudinsa bazai kai hakaba ni dashi nake amfani duk inda nake zuwa”.

Jin hakane yasa ta gane ashe mgnar zuci da tayi ya fito fili.

Innayi kuwa kai ta jinjina tare da cewa.

“In sha Allah dai ba abinda zai gagara”.

Abba kuwa cikin nitsuwa yace.

“Kayan lefenta kuwa nasa matar aminina Dr Ahmad zata haɗa komai, wata ƙil ya iso kafin muje”.

Da sauri innayi tace.

“A’a a barsu sai munje can mu haɗa ai tunda zamuje da zuriyarta duk zasu gani”.

Da sauri Ummu tace.

“Ayi haka kuwa innayi a tafi da amarya ba lefe, ai za’ayi ta surutai”.

Cikin jinjina kai innayi tace.

“Barsu suyi lokacin sune”.

Nan suka ci-gaba da tattaunawa yadda komai zai wakana.

Tun daga wannan rana suka fara shirye-shiryen biki babu kama ƙafan Yaro.

 

Aranan da daddare aka kawo kayan Auren Amina kaya sunyi kyau sosai su Hajiya Lami ne suka tarbi kayan Auren Bayan anwatse Amina ta kalli Samira dake gefenta tayi tagumi wacce baki ɗaya ta rame ta sauya ta dawo shiru-shiru.

Kallon Samira tayi kana tace.

“Samira wallahi da gaske kin fara wari dan ina jin warin”.

Cikin zubda hawaye Samira ta kalleta Muryanta na rawa tace.

“Allah Amina kina ji ko?”.

Kai Amina ta gyaɗa cikin gaskiya da tace.

“Wallahi Ina ji Amina sai kinji kamar warin Baragurbin ƙwai”.

Cikin raunin murya tace.

“Na sani dole za aji warin kawai Mommy na Idan na faɗa mata sai tace bata ji amma nasan dole za aji warin”.

Yamutse fuska Amina tayi kana tace.

“Gaskiya dai kam kina warin Baragurbin ƙwai wallahi ki dage ki koma wajen Boka ya baki magani”.

Kai Samira ta Girgiza.

Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya ta shigo Harara ta watsawa Amina tace.

“Ke dai Wallahi Amina baki da hankali amaimakon ki kwantar mata da hankali sai ki ƙara tayar mata”.

Baki ta tura tare da kallon Hajiya Bunayya tace.

“Mommy wannan ba maganar tada hankali bane gaskiya ne kawai ku koma wajen Boka Kar’uzu yayi ƙoƙarin nemo mata magani”.

lokacin kuma Hajiya Lami ta fito daga toilet dake Bedroom din tace.

“Boka Kar’uzu har yau bai dawo ba daga tafiyar da yayi nima jira nake ya dawo Inje ko shekara jiya naje ban same shiba.

Cikin rauni Samira ta kallesu muryanta na rawa tace.

“Ni dai da an haƙura da neman Magani awajen Boka Kar’uzu kawai anema min maganin Islamic medicine ko Allah zaisa adace”.

Atare Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka ce me kike faɗa haka ki dai bari asake gwadawa agani.

Shiru tayi ba tare da tace musu uffan ba.

 

*Morocco*

 

Motar Moddibo ce tsaye abakin Mouley Yussef Hospital Rabat kusan kullum sai yazo amma da zaran security dake bakin gate din ya ga shine zai ki buɗe masa yau kwana biyu kenan yana sintirin zuwa cikin sanyi jiki ya juya ya koma gida yana so ya faɗawa Abba to amma ta ina zai fara faɗa masa zaice Jameel ɗinsa ko kuma yaya zuwa wannan lokacin hankalinsa ya gama tashi ya rasa shin wani irin tunani zaiyi cikin wannan tunanin ya koma gida.

Washe gari: alhamis haka ya tashi cikin matsanancin kasala saboda yanda aka kwana ana zuga ruwan sama gari yayi sanyi cikin damuwa da ciwon kasala da jin bugun zuciya ya kwana adaddafe ya tashi ya shirya kai tsaye Company ya nufa ya dudduba aikin da akayi zuwa yanzu gaba ɗaya angama daddasa Injinan da za ayi aiki dasu alissafinsu Insha Allah ranan Monday za afara bubbuga Nauikan, Abaya, Laffa, Jallabiya, Sallayu, blankets, Jakankuna, takalma za a cigaba da sarrafa kaya.

Kai tsaye motarsa ya shiga har ya nufi gida sai kuma ya sinci kansa da juya alamar motarsa  kai tsaye Mouley Youssef Hospital Rabat ya nufa yana isa bakin gate ɗin dai-dai lokacin da security ya buɗe wa wata mota gate wannan damar Moddibo ya samu yayi saurin cinna hancin motarsa ciki.

 

Yana isa yayi Parking security na ganinsa yace.

“You again”.

Iya abinda ya iya faɗa kenan domin haiba da ƙwarjinsa yasa ba zai iya korinsa ba cike da nutsuwa Moddibo ya nufa cikin reception duk ido mutanen da Norses ɗin suka zuba masa suna kallon baiwar kyau nutsuwa da kamala da kuma ƙwarjini da yake dashi.

 

Kai tsaye Office ɗin Dr Jameel ya nufa yana isa yayi Knowking ahankali idanunsa suka sauƙa akan Dr Jameel dake tsaye Atsakiyar office Rungume da wata Norse Yana kissing din sassan jikinta cikin sauri ya runtse Idanunsa tare da faɗin.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin,J wai wani irin sauyi ne yazo maka arayuwar ka”.

Yayi mgnar cikin cushewar tunani duk da ɗabi’in wanda ake kira da Dr Jameel suna bashi cikekken yaƙinin cewa ba J dinsa bane wannan tsananin kamanceceniya ne. Toh amman kamanin da hatta muryarsu mgnar tafiyarsu komai iri ɗaya ne da na J ɗinsa yasa ya kasa amincewa kansa cewa ba J ɗinsa bane wannan.

Cikin fushi Dr Jameel ya ɗago kansa ya kalli Moddibo kana yace.

“Wai kai wani irin mutum ne tunda nace maka ba J ɗin da kake nema bane ka barni mana Meyesa zakayi ta bibiyar rayuwata?”.

Cikin sanyi Moddibo ya kallesa kana yace.

“Kaji tsoron Allah J! Shin wace irin rayuwa kasa kanka aciki J!? J mata ka fara bi ka maida kanka kamar kare wanda baisan abinda yake ba J yada ilimin ka zaka maida kanka haka cikin fushin Ubangiji kake so ka faɗa”.

Cike da ɓacin rai Dr Jameel  ya juya ya kallesa kana yace.

“Anyi ɗin idan kana da iko ka hana nace maka Ni ba J ɗin ka ba kabarni inji daɗin rayuwata mana, jikinka ko jikina rayuwarka ko rayuwata matane dole in bisu inji daɗin rayuwata yoh akwai abinda ya kaisu daɗi ne”.

Cikin takaici Moddibo yace.

“J baka ji tsoron Allah ba da bakinka kake jaddada min aikin ka cewa zina kakeyi?”.

Harara Dr Jameel ya watsa masa cike da gadara yace.

“Anyi ɗin”.

Dafe kai Moddibo yayi tare da faɗin.

“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

Cike da takaici Dr Jameel ya fisgo Norse din Wacce da alama ba musulma bace yana janyota ya manna bakinshi da nata.

Cikinta sauri Moddibo ya runtse Idanunsa da ƙarfi ya kifa kansa da jikin bango yana karanta duk wata addu’a da tazo bakinsa cikin sauri ya juya ya fita cikin motarsa ya zauna kasa tabuka komai yayi sai hawaye dake kwaranyo masa cikin ransa yace.

“Na gamsu wannan ba J na bane haƙiƙa ba Jameel ɗin Ummi bane.

Amman wallahi nayi al’ƙawarin in Sha Allah, zan gyara masa rayuwarsa da yardar Allah zai zama tamkar J dina na baya in sha Allah zaici albarkacin kamaninsa da J ɗina”.

 

Dr Jameel kuwa bayan sun gama aikata masha’arsu da wannan Arniyar ya shiga toilet yayi wanka yana fitowa yaji wayarsa na ringing Yana ɗaga wayar yayi Picking tare da kaiwa Kunnensa cike da girmamawa yace.

“Hello Unclee da kanka kuma?”.

Shiru yayi na wasu sekonni sai kuma yace.

“Toh shikenan ba matsala yanzun nan kuwa ganin zuwa.

Yana katse kiran ya gyara   rigarsa tare da gyara zaman Necktie wuyansa.

 

Juyawa yayi ya kalli Norse din cikin bada umarni yace.

“Idan kin gama ki gyara min office ki rufe”.

Cike da yauƙi tace.

“Ok sir”.

Yana fita yashiga motarsa yaja.

 

Cikin sauri Moddibo dake zubda hawaye yabi bayansa duk inda ya juya akalar motarsa nan Moddibo yake bi shi kansa Moddibo baisan inda zaije ba kuma baisan me zaice masa ba, kuma baisan abinda zaiyiba.

 

Amman haka nan yaji wani irin amintaccen nitsuwa da salama a ranshi.

Haka nan yake jin farin ciki, tafiya mai nisa sukayi kafin suka wuce Sheikh Zayed hospital tafiya kamar na kimanin minti goma suka yi suka isa Fadar masarautar ƙasar Marocco baki ɗaya.

Ta cikin jahar Rabat suna isa Dr Jameel Yayi Hong ganin motarsa yasa aka buɗe masa gate ɗin.

farko yana shiga Moddibo ya mara masa baya tare da rumtse idanunsa da ƙarfi sabida harbawar da zuciyarsa tayi kamar zata haɗin ƙasa. Da sauri ya kuma buɗe idanunsa tare da sauƙesu can sama kan tambarin masarautar.

Lokacin ɗaya yaji jikinsa ya fara tsuma, kana duk tsikar jikinsa ta miƙe tsaye.

Da sauri ya kutsa kai cikin tare da bin Dr Jameel bamba to bamba yana shiga yaji zuciyarsa ta buga da Masifaffen ƙarfi wani irin tsuma yaji jikinsa nayi amaimakon yabi motar Dr Jameel da kallo sai ya kuma bin Cikin masarautar Da kallo daga kan dogon ginin zuwa shimfiɗeɗɗen kwalta da kuma yanda tsarin yake baki ɗaya ginin zagaye yake da bishiyoyin dabino ta ko ina masu tsawo, da sukayiwa illahirin ganinsa ƙawanya.

Ahaka suka isa wani babban gate Dr Jameel yayi hong aka buɗe masa yana shiga Moddibo ya mara masa baya.

Shi kuwa Dr Jameel sabida wayar da yakeyi yasa hankalin sa baya kai kan Modibbo ba.

Sassayyan numfashi Modibbo ya saukeganin yadda hadiman ke zirya da hidima.

Yayinda su kuwa

Fadawa da hadiman basuma ga fuskarsa amman a zatonsu tare yaje da Dr Jameel shiyasa basu hana shi shigaba.

 

Suna shiga gate na biyu suka isa dai-dsi kan  wani RounAbout mai masifar kyau tsakiyar farfajiyar fadan. Yayinda hanyoyi guda huɗu suke zagaye dashi, kana gefe-da gefen ko wacce hanya bishi yoyin yan gajjerun dabino ne, masu ɗauke da yaya ringis a kai.

Kana tsakanin, wanda yake miƙe da ta inda su Modibbo suka fuskanta kuwa wani babban baranda ne wanda yake da staps goma sha biyu, a staps ɗin forko Hadimai ne, guda biyu gefen hagu da damansa, sai kuma a steps na shida suma hadi mai biyu sai ana sha biyu su kuma hadimai bibbiyu ne hagu da dama, wata babbar ƙoface mai kyan gani da daukar hankali da kuma taswirar manomi a cikin kekkyawar gona.

Daga nan cikin RounAbout ɗin kuwa a yalwace yake da shuke-shuke na dukkan samfurin kayyakin da ƙasar suke nomawa kasancewarsu manomane, daga tsakiya kuma

Mutun butumin wani ingarman Doki da linzaminsan cikin ado na ƙawa kasan dokin kuma zagaye yake da Grass Capet sai kuma mutum-mutumun mutane biyu da fatanya a hannunsu sai na ɗawisu a gaban dokin.

Sai kuma ƙanan tituna da suka rabu kusan kashi takwas da alamu duka cikin Masarautar yake daga saman RounAbout ɗin anrubuta Barka da zuwa Masarautar Mouley da Larabci.

Daga gefe Dr Jameel Yayi parking yana Parking ya fito shima Moddibo ahankali ya ziro ƙafarsa ya taka ƙasa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafa ƙahon zuciyarsa sabida jin yadda tsikar jikinsa ya tashi yammm tamkar wanda aka watsawa ruwan ƙankara atsakiyar hunturun sanyi.

Cikin sauri Dr Jameel ya juya ya kallesa cike da mamaki yace.

“Yah Salam biyoni nan kayi bawan Allah Meyesa zaka bini har nan? Kasan inane nan kuwa? kasan meya kawo ni nan? kasan me nazo yi? Nace kama san ina ne nan kuwa? Nanfa ba cikin asibiti bane”.

Moddibo kuwa kasa cewa komai yayi saboda yanda tsikar jikinsa ke tashi baki ɗaya ya rasa yanda zaiyi sai kawai ya ƙanƙame jikinsa yana karkawar tamkar mazari.

Cikin sauri Dr Jameel

ya juya banyansu jin wata murya cikin karaji na cewa.

“Jama’a ku lura *Rinƙas* ya kunce ina Sarkin dawakai yake? *Rinƙas* ya kunce jama’a ku kauceeeeh”.

Cikin tsanani  sauri fadawa da sauran jama’a dake zirya a tsakikar suka fara mannewa a jikin bishi yoyin dabinon domin sanin irin gagarumar illar da Rinƙas keyi a duk sanda ya kubce kuma babu mai iya sarrafa shi cikinsu sai sarki Dawaki ko Mai martaba Youseep Mouleey da kansa.

 

Moddibo kuwa jin yadda ake gudu da kuma ganin yadda kowa ke neman mafaka ne yasashi cewa *Rinƙas*

Yayi mgnar a fili a cikin ransa kuma ya kuma sake cewa.

“Rinƙas a na”.

Yayi mgnar tare da saurin juyawa sabida jin wani irin takun aukuwar ingarman doki lafiyeyye ya nufo kanshi gadan-gadan yana wani irin gigitaccen suƙuwansa da harba iska tare da barbaza gezan kwataccen dogon gashin dake kan wuyansa.

Gab-gagab Gab-gagagab Gba-gab, ya nufosa haiƙan ƙadaran.

Dr Jameel kuwa wani irin gigitaccen kara ya sake tare da artawa a guje, ya nufi kam ƙofar fadar.

 

Yayinda gaba ɗaya hadimai da bayi kuwa duk suka ɗaɗdaura hannayensu a kai tare da rumtse idanunsu baki ɗaya sabida gaba ɗaya sun gama sadaukarwa sai dai a dauke nuƙurƙushesshen gawar Modibbo.

 

Shi kuwa Modibbo juyawa yayi ya kalli gabas da yamma Kudu da Arewa na cikin masarautar gaba ɗaya jama’ar da ke ziryar duk sun manne da jikin bishiyoyin kai kace kadangarune.

Wanda ke gefen damansa ya kalla yadda ya zare ido tamkar zai fiddasu waje.

Bayanshi ya juya ya da sauri jin kukan wani mutun.

Da sauri ya juyo kan zaburarran dokin da yaji an kira da Rinƙas ɗin da yayiwa farin sani a mafarkansa.

 

Sai kuma ya kuma kallon dottijon da kallo ɗaya zakayi mishi kasan cikekken mahaukacine tubran.

 

Rinƙas kuwa wani irin gigitaccen haniniya da sukuwa mai bada sautin takunsa mai jawo hankalin mutane, yayinda daga can baya kuma mai gadin sashin dawakanne ke ihu da kururuwa tare da yin mgn cikin tashin hankali yake cewa Modibbo.

“Ka gudu! Nace ka gudu zai kasheka fa”.

Sai kuma ya ƙara ɗaga murya tare da cewa.

“Sarkim Dawaki taimakon gaggawa”.

 

Dai-dai lokacin kuma Rinƙas yayi wani iri-iri haniniya tare da harbin iska kana ya baza gashin kan wuyanshi tare da zura ƙafafunsa na gaba suka tafi suuuwwwh kan Modibbo.

 

Shi kuwa Modibbo cikin tariyo yanayin da yake rayuwa da dokin a mafarkansa na tsawon rayuwarsa.

Ya ture hular kansa tare da girgiza kansa yayi yadda dokin yayi, kana ya saita ƙwayar idanunsa, cikin tsakiyar idanun dokin.

Tare da ɗaga tafin hannunsa na dama ya saita kan goshin dokin.

Wanda hakan ne kuma yasa dokin sakin wani hargitstsen haniniyar da saida ta ratsa kunnuwan tsarki da tawagarsa dake cikin fadar suna zaman yiwa Sarki Jabeer Nuruddeen Gwadabe sallama dan yau yake shirin komawa Nigeria.

 

Juyowa mai martaba sarki Youssef Muhammad Mouley yayi tare da kallon gefen da Sarkin Dawaki yake tare lunshe idanunsa wanda hakan kaɗai ya wadatar ya gane nufin Sarkin.

 

A can waje kuwa gaba ɗaya jama’ar idanu suka zubawa Modibbo da Rinƙas suna kallon sarautar Allah, shi kuwa Modibbo.

Lumshe idanunsa yayi tare da buɗasu cikin na dokin.

Wani irin ɗaga sawu sama dokin yayi alamun sarawa da kuma cikekkiyar sanayya yayi Modibbo, kana yayi ƙasa dasu a hankali ya manna goshinsa da tafin hannun Modibbo.

 

Shi kuwa Modibbo shafa sumar gaban goshin yayi tare da fesar da sassayyan numfashi.

 

Mutumin dake gefen sane yayi wani irin sake baki tare da furta Yah Salam.

Dan sai lokacin ya samu damar ƙarewa fuskantar Modibbo kallo.

 

Dokin kuwa cikin nuna alamun shaƙuwa da sanayya mai tarin yawa, ya rinƙa karkaɗa jelarsa tare da baza gashin wuyansa da sakin haniniya kana ya fara zaga Modibbo tamkar maiyin ɗawafi.

 

Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen murmushi yake tare da jujjuyawa yana kallon duk inda dokin yayi.

 

Saida ya zagayashi sau uku, sai kuma ya dawo gabanshi.

A hankali ya sunkuyo haka yasa Modibbo sumbatar wuyan dokin.

 

Dai-dai lokacin kuma sarki Dawaki ya buɗe ƙofar fadan ya fito da sassarfa ya fara taka steps din.

 

Shi kuwa Modibbo ɗan buge goshin dokin yayi sai ga dokin yayi ƙasa a hankali ya kwanta tare da karkarɗa jelarsa alamun so yake Modibbo ya hau kanshi.

 

Ya ilahi ya mujibatda’awato. Yah Salam, shine kaɗai abinda gaba ɗaya al’ummar dake kewaye da bishiyoyin suka fara faɗa tare da sauƙowa suka nufo Modibbo.

 

Shi kuwa Modibbo gashin saman wuyan dokin ya kamo tare da ja,

Haka yasa dokin miƙewa tsaye cike da biyayya.

Shiko Modibbon a hankali ya lumshe idanunsa, sai kuma yayi gaba dokin na biye dashi tamkar raƙumi da akala.

Duk da babu linzami a wuyan dokin.

 

Shi kuwa Modibbo ido a lumshe ya juya gefen hagunsa ya fara tafiya yana mai kallon taswirar hanyar inda zaije ya ɗaure dokin na dawo masa filla-filla kamar yadda yake gani a mafarkansa.

 

Wannan al’amari yayi masifar sa mamaki da kaɗuwa a zuƙatan al’ummar waje.

 

Dr Jameel kuwa ido ya zubawa Modibbo.

Yayinda sauran Hadiman kuwa gaba ɗaya hannun suka rinƙa ɗaurawa a ƙirzansu suna ɗan ronƙofowa kaɗan sunayiwa Modibbo wani irin gaisuwar ban girma.

 

Sarki Dawaki kuwa cike da al’ajabi da ta’ajjudin ganin yadda wani ke sarrafa Rinƙas ban ya sani duk duniya shida Abualeey  ne kaɗai ke iya sarrafa dokin wato sarki Youseef, ko Ibrahim Mouley baya matsowa kusa dashi,  kana ya sani  kusan mutum uku ya kashe a cikin masarautar.

 

Hakane yasa ya fara sassarfa, amman ina ya kasa iso Modibbo da dokin domin shima da sassarfan yake tafiya ganin dokin na sonyin sukuwa.

 

Kana gaba ɗaya mutanen kuma yuuuh sukayi suka bi bayan Sarki Dawaki domin al’ajabin wannan al’amarin.

 

Tafiya mai nisa sukayi kana Modibbo yayi kwanan gefen yamma nan ma tafiya mai tsawo sukayi kana suka ɓullo kan wani ƙaton farfajiya wanda a ƙalla dawakai sun kai ɗari uku zuwa huɗu ke wurin.

Duk inda ka wulga idonka iya ganinka dawakaine a wurin. Shi kuwa Modibbo wata yalwatacciyar hanya yabi tare da ratsa tsakiyar dawakan ya wuce.

“Iko sai Allah”. Mutumin nan dake ya shelanta tsinkewar Rinƙas da gudu ya nufosu tare da maɗaukakiyar mamaki a fuskantar.

 

Shiko Modibbon ratsawa ya rinƙayi har ya isa inda nanne tirken dokin. Ɗaureshi yayi kana ya juyo.

Juyowarsa kuwa itace tasa numfashin Sarkin Dawaki kusan ɗaukewa a fili yace.

“Yah salam”. Sabida  ganin kamannin fuskantar Modibbo tayi masifar girzashi, kawai sai ya ɗaura hannunshi na dama kan ƙirjinsa ya ɗan rusunar da kai, yayinda gaba ɗaya sauran ma haka sukayi.

 

Shi kuwa Modibbo ratsasu yake a hankali tare da bin hanyar da bata nan ya zo ba,  tafiya kaɗan yayi ya ɓullo kan fadar.

Wanda tuni wasu hadiman sun kuma maye gurɓin waɗancan da suka tafi wurin dokin.

Jiyo alamun takun mutanene yasa ya ɗan juyo, ainkuwa zugar tawagar da ya barine suke biye dashi cike da girmama.

Bai fahimci komaiba a cikin abinda suke mishi, kawai dai yana bin hanyoyin da ya saba gani a mafarkansa ne, hakan yasa ya fara taka steps ɗin.

Da sauri wanda yake bakin ƙofar ya tura ƙofar tare da sa hannun sa ɗaya a ƙirji ya ɗan rusunar da kai, ɗai hannun kuma yayi masa alamun bismlillah ga hanya ka shiga.

 

A hankali yake takun cike da kamala da haiba, ya kutsa kanshi cikin tamfatsestsen falo na al’farmar da ƙasaita. Wanda komai na cikinsa ja ne, sai ratsin baƙi, bisa alamu kalan tutar ƙasarsu ce.

 

Babban falone wanda a ƙalla zai iya ɗaukan mutun sama da ɗari.

Yana shiga Sarkin Dawaki na biye dashi a baya.

Da sauri ya kalli gefen damanshi jin muryar yaron nan da suka haɗu a jirgi na cewa.

“Alhamadullah Abeey kaga ga wanda nacema mun haɗu dashi a jirgi, mai kama da Ibrahim”.

Faɗin hakane yasa duk suka kalleshi sai kuma suka kalli inda yake nuna musu.

Da sauri wani Kekkyawan Mutun mai cikar haiba, kamala, haɗi  da ƙasaita ya miƙe tsaye cikin shiga ta al’farmar dake nuni da shine Sarkin masarautar ƙasar Marocco.

Miƙewarsa tsayence tasa dukkan sauran mutanen kama daga Waziri, Galafima, Wambai, Ɗan Maliki, Sarkin gida, Sarkin fada, dama gyara kimtsi Sarkin zagi kab suma suka miƙe tsaye cike da zubawa Modibbo idanu tamkar zasu ɗagashi sama da idon.

Dr Jameel kuwa, muƙut ya haɗiye wani yawu mai haɗe da mmki dan jarabar neman mata shi bai barshi yayi wani tunani kan kamannin Modibbo da Ibarahim ba koma yace da kawunshi ba.

Sai kuma yace.

“Har nan”.

Moddibo kuwa Jabeer bin Jabeer daya dawo gabanshi yana miƙa mishi hannu ya zubawa ido tara da bashi hannun.

 

Shiko Jabeer jawoshi yayi har zuwa gaban Sarkin tare da cewa.

“Ganshifa ko makaho ne ya shafa fuskarsa ya shafa taka ko ta Ibrahim yasan wannan mallakinmu ne shi, Abeey ba dama na gaya makaba”.

Ya ƙare mgnar da kallon Sheikh Jabeer .

Shi kuwa Sheikh Jabeer wani Gwauron numfashi ya fesar tare da yiwa Ɗan aminin nashi nuni daya zauna.

Cike da kaɗuwa Sarkin Mouleey ya zauna kana yayiwa dukkan fada alamun su zauna.

Haka kuwa duk suka zauna.

Dr Jameel ne ya ɗanyi gyaran murya tare da rusunar da kai cikin ladab yace.

“Ayi min izini in tashi zan shiga wurin Didi in duba Rahman”.

kai Sarkin fada ya gyaɗa masa tare da nuna masa hanya alamun yaje.

Cikin sauri Dr Jameel ɗin ya miƙe da tare da kamo hannun wani ɗan yaron da bazai gaza shekara gomaba yace “Muje”. Ya ida maganar tare da jan hannunsa suka juya zasu fita.

Da sauri Modibbo ya miƙe tare da bin bayan Dr Jameel.

Cike da mmki ya tsaya ganin fadawan da suka zagayeshi da sauri kana sunkayi mishi zobe tare da baza manyan rigunansu.

Suka tareshi baya iya ganin Dr Jameel.

Cikin sanyin murya yace.

“Yah haka Ku buɗe min hanya mana zan tafi”.

Da sauri ya juyo jin Muryar Sarkin Zagi na cewa.

“Gyara kimtsi bisa umarnin mai martaba kuyi mishi jagora sashi na musamman”.

Kafin ya fahimci mai kalaman Sarkin zagin ke nufi, sai ji yayi anja hannunsa ba tare da an cire ƙawanyar da ankayi masaba, yaji sun fara tafiya dashi.

“Ikon Allah wai na zaune ya daɗi”.

Shine abinda yake faɗi a ransa yana mai ƙoƙarin ɗago kanshi sama, wai ko zai samu yaga gabanshi amman ina.

A hankali ya fesar da numfashi sabida tariyo masa da mafarkansa da kwakwalwarsa tayi masa.

Taku yaci gaba dayi da bin sawun Sarkin gida dake jansa wanda ta cikin ƙaton falon sukabi ta wata babbar ƙofa, tafiya mai tsawo sukayi kana yaji sun fara hawa steps jim kaɗan kuma yaji sun ɓulo ta wata kusurwar, ɗan gajeren tsaki yaja.

sabida jin tafiyarfa taƙi ƙarewa, kuma mutumin nan yayi mishi riƙon babban ɓarawo, ga ƙattin fadawa da suka zagayeshi.

“Toh wai me haka”.

Ya faɗa dai-dai lokacin da yaji, an ajiyeshi bisa wata ƙasaitacciyar kujera.

Sai kuma yaga duk sun janye ƙawanyar da sukayi mishi kana suka juya suka fita.

Da ido ya rakasu har suka je bakin ƙofa ga mmkinsa sai yaga mutumin nan da ya riƙo hannunsa yaja ƙofar da ƙarfi ya ruf….

 

 

Muje zuwa, wasa ya jiƙa, karatu dan aka biya kuɗin laranra Littafin yafi ɗadi ba haƙƙin kowa a kanki 1k ne fa kacal ki biya kada ki kiranta na sata 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 ki biya in tura miki littafin ki karanta abinki cikin Salam kana in saki a Group ɗin littafin kusha comments,

 

 

Tallah !! Tallah !!

 

Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce  ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* , yau ta sake dawo muku Domin tallata muku Littafin mai Suna ( Rai Daya Jan Zaki)  littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n’a cika Ku da surutu ba  Hausawa sukace Gani yakori ji.

 

Farashin wannan littafin Naira Dari biyar ne 500 kacal  postin biyu a arana  banda ranar Juma’a .

Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.

Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank

Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.

By

*GARKUWAR MARUBUTA*

Leave a Reply

Back to top button